Ganduje Ya Yi Watsi Da Rahoton Kwamitin Buhari

0
439
Rabo Haladu Daga Kaduna

 

GWAMNAN jihar Kano , Abdullahi Umar Ganduje, ya musanta rahoton gwamnatin tarayyar da ya gano cewa cutar korona ce ta yi ajalin kashi 50 zuwa 60 cikin 100 na mutanen da suka mutu a baya bayan nan.

A wata sanarwa da ya fitar, Abba Anwar, mai magana da yawun Gwamna Ganduje, ya ce kwamitin da gwamnatin jihar ta kafa domin yin bincike kan mace-mace ya gano cewa kusan kashi goma sha shida cikin dari ne suka mutu sanadin korona.

Gwamnan ya ambato kwamitin yana cewa: “Mutum 255 cikin 1604 da suka mutu, wato kashi 15.9 ne suka mutu sanadin cutar korona. Wasu daga cikin mace-macen suna da alaka da rashin samun magunguna da kuma dakatar da harkokin rayuwa da na kasuwanci saboda fargabar annobar korona.”

A makon jiya ne Ministan Lafiya Osagie Ehanire ya bayyana wa manema labarai a Abuja cewa binciken da tawagar gwamnatin tarayya ta gudanar game da ƙaruwar mace-mace a jihar Kano ya nuna cewa mutum 979 ne suka mutu a kwanan nan sanadin mace-macen da ba a saba gani ba a jihar.

A cewar ministan, an samu rahotonnin mutuwar ne a ƙaramar hukuma takwas na cikin birni a watan Afrilu.

Ya bayyana cewa an riƙa samun mutuwar mutum 43 a kullum lokacin da cutar na kan ƙololuwarta kafin daga bisani adadin ya zama mutum 11 a kowacce rana.

A watan Afrilu Shugaba Muhammadu Buhari ya aika kwamitin na musamman zuwa Kano don gano sanadin yawaitar mace-macen, sannan ya sanya dokar hana fita ko da yake daga bisani Gwamna Ganduje ya kyale mutane su ci gaba da fita a wasu ranaku

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here