Korona Bairos: An Kirkiri Fasaha Mai Magana Da Hausa

0
488
Sheikh Dr Isa Aliyu Pantami, Ministan Ma'aikatar Kimiyya Da Fasaha

Rahoton Z A Sada

WASU matasa dalibai ‘yan asalin arewacin Najeriya da ke karatu a jami’ar Imperial College da ke birnin Landan sun kirkiri wata fasaha mai tunani irin na dan adam da suka yi wa lakabi da suna Amina.

Fasahar wadda ta ci sunan sarauniya Amina ta Zazzau na amsa tambayoyi ne a harshen Ingilishi da na Hausa dangane da bayanai da suka shafi annobar korona.

Al-Amin Bugaje

Amina dai ba batun-butumi ba ce wato mai zati irin na dan adam, fasaha ce mai kwakwalwar dan adam da ake tattaunawa da ita a kan intanet da ake kira ‘chatbot’.

Za a iya cewa Amina ce fasahar bot irinta ta farko da aka kirkira da harshen Hausa.

Al-amin Bugaje wanda daya ne daga cikin wadanda suka kirkiri wannan fasaha, ya shaida wa BBC cewa “abu na gaba da muke son yi shi ne samar da damar aikewa da sakon murya ga Amina maimakon rubutu.”

Ya kara da cewa “mun kirkiri Amina ne domin bai wa masu magana da harshen Hausa gudunmowa dangane da bayanan da suka shafi annobar korona.”

To sai dai da aka tambayi Bugaje kan ko akwai yiwuwar samar da butum-butumi na Amina sai ya ce “abin da kamar wuya a samu hakan a nan kusa sai dai nan da wasu ‘yan shekaru.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here