Sarkin Daura Ya Sauya Fasalin Majalisar Hakimai

0
585
Daga Usman Nasidi. 
MAI martaba Sarkin Daura, Dakta Umar Farouk, ya gudanar da sauye-sauye ga wasu Hakimansa domin inganta zaman lafiya da hadin kai a masarautar. Kakakin masarautar, Malam Usman Ibrahim, shi ne ya tabbatar da hakan ga manema Labarai a ranar Laraba, a fadar Daura. Malam Ibrahim ya ce an daga likafar Sarkin Tsaftar Daura, Alhaji Lawal Usman zuwa mukamin Kauran Daura, wanda a yanzu ya shiga cikin sahun masu zaben sarki a masarautar. Haka kuma an bai wa Sarkin Sudan, Alhaji Yusuf Nalado, kujerar babban mashawarci na musamman ga Sarkin Daura. A cewar kakakin Masarautar, Sarkin na Daura ya nemi hakiman da aka daga likafarsu da su jajirce wajen yin aiki na aminci da adalci sannan kuma su kawo zaman lafiya da hadin kai. Sarkin ya kuma hori ‘yan majalisar da su dage wajen kwarara addu’o’i na neman zaman lafiya da hadin kai a daukacin jihar Katsina da kuma kasa baki daya. A yayin haka Sarkin ya kuma yi kira ga al’umma da su tabbata suna yin biyayya ga dukan Hakimansu na yankunansu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here