Dalilin ‘Yan Sanda Na Kama Shugaban Waɗanda Suka Yi Zanga-zanga A Katsina

0
817
Rabo Haladu Daga Kaduna
GAMAYYAR Kungiyoyin Arewacin Najeriya,Coalition of Northern Groups (CNG), ta ce rundunar ‘yan sandan  ta kama Nastura Ashir Sharif, shugaban kwamitin amintattunta saboda zargin ya zagi Femi Adesina, mai magana da yawun Shugaba Muhammadu Buhari.
Mai magana da yawun gamayyar kungiyoyin, Abdul-Azeez Suleiman, ya shaida wa manema labarai ranar Laraba cewa an kama Ashir Sharif bayan sun kammala zanga-zanga a birnin Katsina inda suka yi kira a ɗauki mataki game da kashe-kashen da ke faruwa a yankin.
Ya ce an tafi da shi hedikwatar rundunar da ke Abuja,  inda yake tsare yanzu haka.
Sanarwar da suka fitar tun da fari ta ce “kungiyar CNG ta yi matuƙar kaɗuwa ganin cewa gwamnatin da ke iƙirarin kare mulkin dimokradiyya za ta iya hantarar mutanen da suka fito don kare nauyin da ƙundin tsarin mulki ya dora musu”.
Masu zanga-zangar, mai taken#ArewaIsBleeding a turance, wato ‘Jini yana kwarara a Arewa’, sun bayyana matuƙar ɓacin ransu kan halin ko-in-kula da suke zargi gwamnatocin kasar na yi kan yawaitar kashe-kashe a yankin.
Sun ce za su gudanar da irin wannan zanga-zanga a jihohi 19 da ke arewacin don matsa lamba ga gwamnati ta ɗauki matakin da ya dace kan masu kashe-kashen.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here