Kawunta Dan Boko Haram Ne Ya Mayar Da Ita Ganimar Yaki

0
337

Rahoton Z A Sada

YAYIN da Majalisar Dinkin Duniya ta ware ranar 19 ga watan Yuni domin yaki da cin zarafin wadanda tashin hankali ya shafa a fadin duniya, a Najeriya wata baiwar Allah da aka boye ko sakaya  sunanta ta shaida wa kaffar yada labarai ta BBC cewa “‘yan Boko Haram sun ci zarafin mu inda suka yi ta tarawa da mu.”

Wannan matashiya dai ta shaida wa BBC irin yadda lamarin ya faru da ita lokacin da ‘yan kungiyar Boko Haram suka kai hari a garinsu.

Ta ce ” ranar wata Talata sai ‘yan Boko Haram suka shigo garinmu suna kabbara inda suka karbe garin suka kuma kashe duk maza sannan sai suka kada duk mata zuwa daji bayan sun kone gari.

A ranar kawuna wanda kanen mahaifina ne ya zo ya ce na tashi na bi shi ni na zama ganima, inda ya tafi da ni kuma ya yi ta tara wa da ni.”

Matashiyar ta kara da cewa “daga baya ne ‘yan Boko Haram din suka kashe kawun nawa inda aka aura min wani daban.

Mun samu mun tsere ne daga hannunsu a wani dare da misalin karfe daya na dare saboda lokacin ne suke yin bacci.”

To sai dai matashiyar ta ce duk da sun samu tserewa daga hannun ‘yan Boko Haram, sun fuskanci wulakanci da tsangwama a sansanin ‘yan gudun hijra da ke Bama inda aka kai su.

“Duk inda muka yi a sansanin sai ka ji ana nuna mu ana cewa ga matan ‘yan Boko Haram. Ni dai abin da Boko Haram ta yi min ba zan taba yafewa ba musamman kawuna wanda ya lalata min rayuwa ba zan taba yafe masa ba.”

Cin zarafin Boko HaramHakkin mallakar hotoGETTY IMAGES

Daga karshe wannan matashiya ta samu ta koma makarantar sakandare, inda kuma yanzu haka take da burin zama sojar sama domin yakar Boko Haram.

“Burina yanzu na zama sojan sama domin na hau jirgi na tarwatsa ‘yan Boko Haram. Zan so a ce Boko Haram ta kare a Najeriya”, in ji matashiyar.

Yanzu dai matashiyar tana makaranta sannan tana koyon sana’ar dinki a wata cibiyar agaza wa masu gudun hijra.

Sai dai wannan baiwar Allah ta ce tun lokacin da kawun nata ya yi awon gaba da ita, ba ta daina zubar da hawaye ba har sai da ta hadu da cibiyar Al-ameen Foundation.

Majalisar Dinkin Duniya dai ta kebe wannan rana ne ta 19 ga watan Yuni da zimmar nusar da al’umma bukatar daina cin zarafin mutanen da suka fada cikin tashin hankali.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here