Ku Yi Watsi Da Rahotannin Mutuwar Ajimobi – Kakakinsa

0
383

Daga Usman Nasidi.

TSOHON Gwamnan jihar Oyo sannan mataimakin shugaban jam’iyyar APC, Abiola Ajimobi, bai mutu ba, a cewar kakakinsa, Bolaji Tunji.

A cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na ‘Facebook’ a daren ranar Alhamis, Tunji ya bukaci jama’a su taya maigidansa da addu’a.

“Ku yi watsi da zancen mutuwarsa, duk jita – jita ce kawai. Mu ci gaba da addu’a ,” kamar yadda Tunji ya wallafa.

An yada labarin mutuwar Ajimobi a dandalin sada zumunta na Tuwita.

Kazalika, kafafen watsa labarai da dama sun wallafa rahoton mutuwar Ajimobi.

Sai dai, jaridar TheCable ta rawaito cewa ta fahimci Ajimobi ya na cikin mawuyacin hali, saboda ya shafe fiye da mako guda a wani bangaren kulawa na musamman a wani asibiti da ke jihar Legas.

Ana zargin cewa Ajimobi ya kamu da cutar korona, kuma yana cikin mawuyacin hali sakamakon wasu cututtuka da ke damunsa.

Lanre Issa-Onilu, sakataren yada labaran jam’iyyar APC, ya sanar da cewa kwamitin gudanarwa na jam’iyya (NWC) ya damka wa Abiola Ajimobi, rikon kwaryar shugabancin jam’iyyar APC.

Kafin nadinsa a matsayin shugaban rikon kwarya, Ajimobi, tsohon Gwamnan jihar Oyo, ya kasance mataimakin shugaban jam’iyyar APC na shiyyar kudu maso yamma.

Duk da Ajimobi ba shi da lafiya, yana killace sakamakon kamuwa da cutar da ake zargin korona ce, kakakinsa, Bola Tunji, ya sanar da cewa tsohon Gwamnan ya bukaci mambobin jam’iyyar su zauna lafiya da juna.

Ayodele Fayose, tsohon Gwamnan jihar Ekiti, ya ce jam’iyyar APC mai mulki ta fada cikin rigingimu ne saboda Allah yana fushi da jam’iyyar.

Jam’iyyar APC ta na fama da rigingimu kala biyu; rikicin zaben fidda dan takarar Gwamnan jihar Edo da tabbatar da dakatar da shugabanta na kasa , Adams Oshimhole, da kotun daukaka kara ta yi.

Bayan APC ta sanar da korar takararsa, Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, ya sanar da yin murabus daga zama mamba a jam’iyyar.

Sa’o’i kadan bayan ya sanar da barin jam’iyyar APC, wata kotun daukaka kara da ke zamanta a Abuja ta tabbatar da dakatar da Oshiomhole daga shugabancin jam’iyyar APC.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here