Atiku Ya Yi Maraba Da Shigar Obaseki PDP

0
283
Rabo Haladu Daga Kaduna
TSOHON mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar shugabancin kasa a jam’iyyar PDP a zaben 2019, Atiku Abubakar, ya yi maraba da Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki wanda ya shiga jam’iyyar ranar Juma’a.
A sakon taya murnar da ya wallafa kan shigar Gwamnan PDP, Atiku Abubakar, ya ce “PDP ita ce hakikanin jam’iyyar al’umma”.
“Ka shigo jam’iyyar PDP ne lokacin da aka sauya fasalinta ta yadda take son aiwatar da mulki nagari domin gajiyar ‘yan Najeriya,” in ji tsohon mataimakin shugaban kasa.
Mr Obaseki ya shiga jam’iyyar ne kwana kadan bayan ya fice daga jam’iyyar APC wacce a cikinta aka zabe si a karon farko.
A makon da ya wuce ne jam’iyyar APC ta ce Obaseki ba zai iya shiga takara a zaben fitar da gwani ba saboda a cewarta akwai banbance-banbance a takardun makarantarsa.
Sai dai masu lura da harkokin siyasa na ganin rikicin ubangida da yaronsa da ke tsakaninsa da tsohon Gwamnan jihar Adams Oshimohle kuma shugaban APC da kotu ta dakatar ne ya yi sanadin hana shi sake takara.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here