Mutum Miliyan 7 Ne Za Su Fuskanci Matsalar Yunwa a Najeriya

0
359

Rabo Haladu Daga Kaduna

CIBIYAR nazarin matsalolin abinci ta duniya ta yi hasashen mutane kimanin miliyan bakwai ne za su fuskanci matsalar yunwa a Najeriya a cikin watannin Yuni da Yuli da kuma Agustan wannan shekara.

Rahotan na nuni da cewar daga cikin rukunin mutanen da za su fuskanci karancin abinci, har da yara kananan wanda za su fuskanci rashin samun abinci mai inganci da zai gina musu jiki.

Ita dai wannan cibiya na fitar da rahotanta a kowacce shekara domin gargadin hukumomi da kuma gwamnatoci su tabbatar sun dauki matakan kwarai don tinkarar matsalar.

Matsalar tsaro a sassan Najeriya da gurbatar muhalli da kuma bayyanar cutar coronavirus na daga cikin dalilan da hukumar samar da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce za su janyo karancin abinci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here