Bai Kamaci A Hada Yanayin Yin Ibadar Musulmai Da Na Kiristoci Ba – Shiekh Abdulhadi Daura

0
388

Usman Nasidi, Daga Kaduna.

WANI babban Malamin addinin Musulunci kuma babban limamin Sallar Juma’a  na Masallacin Marigayi Al-Adamawi da ke Hayin Malam Bello Rigasa Kaduna, sheikh Abdulhadi Aliyu Daura, ya bukaci gwamnatin Jihar Kaduna da ta daina kamanta yanayin yin Ibadar al’ummar Musulmi da na kiristoci domin su an wajabta musu yin salloli biyar a kowace rana.

Sheikh Abdulhadi ya bayyana hakan ne jim-kadan bayan kammala sallar Juma’a a wata zantawarsa da wakilinmu a masallacin Dan Fodio inda ya bayyana cewa yanayin yin Sallar al’ummar Musulmi ba kamar na abokan zamansu kiristoci ba ne domin  su basu da wajibci a kan jin ibadar tasu cikin Jam’i.

Ya kara da cewa Allah Ubangiji ne Ya wajabtawa kowani musulmi yin Ibada na Salloli biyar ako wace rana kuma an fison yin shi cikin Jam’i domin samun ladar kowace sallar, don haka bai kamaci ace don za a bada damar zuwa coci ranar Lahadi saboda haka za a rika bude masallatai ranar juma’a ba kadai.

Ya ce “shi addinin Musulunci, ba wani abu bane wanda wani ya zauna ya tsara don kan shi illa, sako ne wanda Ubangiji Ya aiko da shi ta hannun manzonsa tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, kana aka umarci kowani musulmi da ya yi ladabi, ya yi koyi da irin wannan karantarwa ta shi.”

Acewar sheikh  Daura, idan kuma aka yi la’akari da yawan al’ummar dake Jihar, al’ummar musulmin su suka fi rinjaye da kusan kaso saba’in wanda koda kuri’a za ayi, zasu fi daukar kaso mai rinjaye, toh don haka bai kamata ace ana kamanta su da wasu ba idan za a zartar da wani hukumci.

“idan har za a iya barinmu muzo masallaci yin sallar Juma’a, toh bai kamata ace an dakatar mu daga zuwa yin sallolinmu na kamsul salwat da muke kullum ba domin kuwa anan ne ya fi saukin mu dauki matakin kare kawunan mu, sannan mu sa Ido a akan dukkan wasu al’amura, amma ba wai ace kawai don wasu basa yi ko ba za su yi sai ace muma za a hana mu bayan ansan ba addininmu daya ba.” inji shi

Hakazalika, malamin ya yaba da irin namijin kokarin da gwamnan Malam Nasiru El-Rufa’i yake yi wajen ganin ya dakile kara yaduwar cutar korona biros wacce annobar ta zama ruwan dare game gari kuma har ta kaiga dakatar duk wasu al’amura na duniya baki daya.

A karshe, Sheikh Abdulhadi Daura ya kira ga gwamnatin Jihar da ta sake duba yuwar barin al’ummar ta musulmi dasu cigaba da yin Ibadunsu yadda ya dace a masallatai domin yin hakan zai kara taimakawa wajen neman sauki na kawo karshen cutar ta hanyar yin addu’o’i ayayin gudanar da Ibadun.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here