Ruwan Sama Da Iska Mai Karfi Ya Rusa Gidaje Da Dama A Garin Rigasa Kaduna

0
293

Usman Nasidi, Daga Kaduna.

A SAKAMAKON wani ruwan sama da Iska mai karfin wanda gudana a daren ranar Lahadi da misalin karfe goma zuwa sha dayan dare, ruwan ya yi sanadin tsugunar da wasu al’’umma da dama inda ya bar su chako-chako a kan hanyoyi da cikin unguwanni da ke babbar kwaryar garin Rigasa Kaduna.

Al’amarin wanda ya gudana a cikin ‘yan lokutan kadan wanda bai wuci ‘yan mintuna talatin ba na dadewar ruwan kamin ya tsagaita, ya yi sanadin kawo rudani da tagumi a cikin kwaryar garin yayinda jama’a da dama suka rasa ta cewa don rashin sanin abun yi da inda zasu kwana.

Wakilinmu wanda ya kai ziyarar gani da ido a cikin daren, ya tarar da al’umma a cikin garin a wurare da dama a tsatsaye chako-chako yayinda wasu ke ta kokarin yin wasu yan aikace-aikace don ganin sun kawar da sauran wasu kayayyakin su masu sauran mahimmanci da amfani.

Ruwan saman da Iskar mai karfin gaske daya gudana, ya yi sanadin raunata wasu yara hudu almajirai wanda aka garzaya dasu asibiti mafi kusa don duba lafiyarsu a sakamakon tugewar wata babbar bishiya wacce ta afkawa gidan da suke.

Hakazalika, ruwan da iskar ta yi sanadin rushewar wasu katangu, gidaje, chiben-chiben wutan lantarki dana fitilun haska hanya, yayewar kwanukan gidaje ciki har dana wani gidan kamfanin siminti, tugewar wasu manyan bishiyoyi yayinda wasu suka afka kan wasu gidaje kana wasu akan hanyoyi.

Wasu al’ummar da dama musamman mata da yara, sun kaurace wa gidajen nasu don neman wasu wuraren da zasu kwana a sakamakon ambaliyar da ruwan ya yi a cikin gidajensu nasu, kana da ruguza wasu sassan ko yaye kwanukan gidajen nasu baya ga lalata dukiyoyi masu tarin yawa.

Kawo izuwa lokacin damuka kawo muku wannan labarin, majiyarmu ba ta samu rahoton rasa ruyuka ba, sai na asarar dukiyoyi wadanda basu misultuwa. Allah Ubangji Ya kyauta kuma Ya mayar da alheri.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here