Ya kamata A Bude Masallatan Sallolin Kamsul Salwat – Malam Aninu Sautus Sunnah

0
391

Usman Nasidi, Daga Kaduna.

WANI babban malamin addinin musulunci, kuma na’ibin limanin masallacin Dan Fodio da ke garin Kaduna, malam Muhammad Aminu Ibrahim Sautus sunnah, ya yi kira ga gwamnatin Jihar Kaduna da ta duba yuwar bude masallatan Sallolin Kamsul salwat wato na Salloli biyar da ake yau da kullum domin za su fi saukin kulawa wajen rage yaduwar cutar korona bairos.

Malamin ya bayyana hakan ne a wani zantawwarsa da wakilinmu inda ya bayyana cewa masallatan yin sallolin kamsul salwata ne zasu fi saukin kula da al’amarin muddun har idan za a iya amincewa da bude masallatan Juma’a wanda al’umma ke yin tururuwa zuwa yin sallah.

Ya kara da cewa tabbas wannan annoba ta korona biros wata babbar al’amari ce wacce ya kamaci a lura da ita duba da irin yadda ta addabi duniya baki daya har da manyan kasashe irinsu amurka da china wadanda ke kan gaba wajen kere-kere da fasaha.

Ya ce “idan muka dubi wadannan masallatan, za kuga a duk lokutan yin sallolin jama’a basa taruwa dayawa tamkar yadda muke taruwa a lokutan yin sallar Juma’a saboda a lokutan yin sallolin a wasu masallatan, mutane basa wuce mutum ashirin zuwa hamsin wadanda suke halarta ba.”

Acewar Malam Aminu Sautul Sunnah, idan har za a iya daukar mataki a lokutan sallar Juma’a da mutane ke tarewa, toh babu shakka kula da lura da al’amuran al’umma a wajen daukar matakai a lokutan sallolin lamsul salwat zai sauki ga jama’ar idan za ayi sallolin.

“Alalhakika, wannan cutar ta korona biros ba karamar annoba bace domin a tarihi ba a taba kulle masallacin Ka’aba ba sai wannan karon a sakamakon wannan annoba, kuma hakan na da nasa bad a nuna cewa mun bar Allah ne saboda haka komawa ga Allah ne kadai mafita a cikin wannan lamarin.”

Hakazalika, ya kara da jan hankalin ga malamai da sauran al’umma dasu mayar da al’amuransu ga Allah domin wannan annobar na nuni da cewa jama’a sun yi sakaci dayawa ne yasa Ubangiji Ya jarabce su da irin wannan masifar don nuna izzar Shi a gare su.

Malam Aminu, ya bayyana farin cikin sa bisa ga ganin yadda gwamnatin Jihar ta dubi koken al’umma kana ta sassauta dokar ta don barin Jama’a su samu damar halartar sallar ta juma’a wanda aka safe akalla watanni biyu da rabi ba tare da an halarta ba.

A karshe, ya yi kira ga malaman addini da suyi kokarin fadakar da al’ummarsu a kan gaskiya bisa ga ita wannan cutar ta korona biras domin tabbas akwai ta kuma ta mugun illa da hadari ga rayuwar al’umma baki daya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here