Har Yanzu Ba Mu Sa Ranar Bude Tashohin Jiragan Kasa Ba- Ameachi

0
381
Rabo Haladu Daga Kaduna
GWAMNATIN tarayya ta bayyana cewa har yanzu ba ta sanya ranar da za’a bude tashoshin jiragen kasa ba, sai an samu raguwar yaduwar cutar Korona.
Ministan sufuri, Rotimi Ameachi, shi ne ya bayyana haka a shafinsa na ‘Twitter’ inda ya ce har yanzu suna tsara hanyoyin da ya kamata a bi idan za’a bi na dakile yaduwar cutar Korona kamin a bude tashoshin jiragen kasa, a cewarsa, ko da ma an Bude Tashoshin ya zama wajibi duk wani fasinja sai yabi ka’idojin kula da lafiya kamin ya Hau jirgin.

Ministan, ya kara da cewa babu wani fasinja da za su bari ya hau jirgin face ya bi ka’idoji da dokokin rigakafin dakile yaduwar Cutar Korona da ma sauran dokokin da za su shimfida.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here