Za Mu Ci Gaba Da Tafiyar Siyasa Da Kwankwaso- Inji Kwamared Sani Romi.

  0
  455

  Kwamared Sani Isa Romi.

  Jabiru A Hassan, Daga Kano.
  WANI matsahin dan siyasa kuma mai kishin matasan wannan kasa da dorewar dimokuradiyya Kwamared Sani Isa Romi yace zai ci gaba da tafiyar siyasa da tsohon gwamnan jihar kano, Injiniya Dokta Rabiu Musa Kwankwaso saboda kyawawan manufofin sa.
  Yayi wannan bayani ne cikin hirar su da wakilin mu, inda ya sanar da cewa ko shakka babu tafiyar siyasa da Kwankwaso tana da amfani idan aka dubi irin nasarorin da tsohon gwamnan take samu a siyasar wannan kasa tareda kawo sauyi a tsarin jagoranci bisa dimokuradiyya da sanin ya kamata.
  Kwamared Sani Isa Romi ya nunar da cewa yanzu lokaci yayi da al’uma zasu fahimci cewa tsahon gwamnan Kwankwaso jagora ne mai son ci gaba kasa da al’umar kasa kamar yadda aka ga yayi tun shigar sa cikin harkokin siyasa, tareda fatan cewa al’umar Nijeeiya zasu ci gaba da nuna soyayyar su gareshi.
  Haka kuma ya jaddada cewa da yardar Allah, jagorancin da Kwankwaso yake yiwa al’umarsa zai zamo alheri ga wannan kasa tamu, musamman yadda jagoran yake kokarin tabbatar da cewa kowane dan kasa yana jin dadi dukda  irin halin da duniya tà tsinci
  Bugu da kari,Kwamared Sani Romi ya bayyana cewa ya shiga takarar neman zama dan majalisar dokokin jihàr kano daga karamar hukumar Dawakin Tofa domin samun damar taimakawa matasa tareda yin godiya ta musammàn ga daukacin matasan kasarnan saboda goyon bayan da suke nuna wa jam’iyuar PDP walau a birni ko yankunan karkara.
  Daga karshe matashin dan siyasar yayi amfani da wannan dama inda ya bukaci Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso da ya amsa kiran da suke yi masa domin tsayawa takarar ahugabancin kasarnan domin kowa ya hakikance cewa Kwankwaso zai kawo sauyi na gaakiya a wannan kasa tamu mai albarka.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here