Za Su Yi Amfani Da Mafarauta Don Kauda Rashin Tsaro A Arewacin Najeriya

0
336

Rabo Haladu Daga Kaduna

KUNGIYAR Gwamnonin Arewacin Kasar nan sun yanke shawarar samo mafarauta domin taimakawa wajen aikin samar da tsaro a yankunansu.

Daukar Wannan mataki ya biyo bayan ci gaba da kashe-kashen da ake samu a Jihohin Katsina da Zamfara da Sokoto da kuma wasu yankunan arewacin kasar.

Bayan wani taro da Gwamnonin suka gudanar ta kafar bidiyo domin nazarin tabarbarewar tsaron a karkashin shugaban su kuma Gwamnan Jihar Fillato Simon Lalong, Gwamnonin sun bayyana matukar damuwar su kan lamarin wanda ke cigaba da lakume rayukan jama’a da kuma asarar dukiyoyi.

Taron ya amince a kafa wani kwamitin tsaro na musamman a karkashin Gwamnan Jihar Kogi Yahya Bello wanda zai taimaka wajen hada kai da bangarorin jami’an tsaro wajen samun nasarar kawo karshen matsalar.

Sanarwar bayan taron ta ce Gwamnonin sun kuma amince su kafa wani kwamitin tuntuba a karkashin Gwamnan Filato Simon Lalong wanda zai gana da Sarakunan Gargajiya da shugabannin addinai da shugabannin jama’a domin basu damar taka rawa wajen shawo kan matsalar.

Taron ya amince da baiwa kungiyoyin Yan sa kai da mafarauta da Yan banga damar taka rawa wajen tattara bayanan asiri domin taimaka wa jami’an tsaro.

Gwamnonin da suka jajanta wa ‘yan uwa da iyalan wadanda aka kashe ko aka jikkata a hare haren Yan bindigar sun bukaci jama’a suyi hakuri don suna hada kai da gwamnatin tarayya wajen ganin an gaggauta kawo karshen lamarin da kuma tallafa wa wadanda hare haren ya ritsa da su.


LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here