Gwamnatin Filato Ta Yi Barazanar Sake Sanya Dokar Kulle A Jihar

0
307

Isah Ahmed Daga Jos

GWAMNATIN jihar Filato ta yi barazanar sake sanya dokar kulle a jihar, saboda yadda ake karya dokokin kare yaduwar cutar annobar korona a jihar,  da kuma samun karuwar yaduwar cutar, tun bayan da gwamnatin ta janye dokar kulle a jihar. Wata sanarwa da ke dauke da sanya hanun Kwamishinan watsa labaran jihar, Mista Dan Manjang da aka raba wa ‘yan jarida a garin Jos ce, ta bayyana wannan gargadin.

Sanarwar ta ce ganin halayar da mutane suke nunawa na karya dokokin da gwamnatin jihar ta sanya, na kare yaduwar wannan annoba, gwamnatin za ta sake sanya dokar kulle a wuraren da ake karya wadannan dokoki da aka sanya, na sanya takunkumi da wanke hannu da bai wa juna tazara, matukar mutane ba su canza wadannan halaye ba.

Sanarwar ta ce gwamnati ta lura cewa wuraren da suke kan gaba wajen karya wadannan dokoki su ne wuraren ibadu da kasuwanni da tashoshin mota da motocin da suke daukar fasinjoji da ‘yan Keke Napep.

‘’Gwamnatin Filato tana tunasar da al’ummar jihar nan  cewa Gwamnan jihar nan,  Simon Lalong tuni ya bada umarnin a hukumta  duk wanda aka kama  ya karya wadannan  dokoki na hana yaduwar wannan annoba.’’

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here