‘Yadda Kamfanin ‘Yan Indiya Ya Kulle Mu Tsawon Wata Uku A Kano’

0
342
Rabo Haladu Daga Kaduna
HAMZA Ibrahim mai shekara 28 wanda ya kammala karatunsa a Jami’ar Bayero Kano yana daya daga cikin mutum 300 da ‘yan sanda suka ceto daga wani kamfanin shinkafa bayan da suka yi korafin cewa kamfanin ya rufe su tsawon wata uku.
Hamza wanda ya shaida wa manema labarai cewa ya fara aiki da kamfanin mallakin ‘yan Indiya a shekarar 2019, kuma albashinsa naira 28,000 ne, ya ce lamarin ya fara ne a lokacin da aka sanya matakin kulle sakamakon annobar cutar korona.
“Ina daga cikin ma’aikatan da ‘yan sanda suka ceto daga Kamfanin Popular Farms a ranar Litinin, kuma abin ya fara ne a lokacin da aka saka dokar kullen annobar cutar korona, maimakon kamfanin ya bi dokar gwamnati ya rufe, sai kawai suka kira mu suka ce duk mai son zama ya zauna ya ci gaba da aiki tare da alkawarin kara mana naira 5000 a kan albashinmu. Wannan dalilin ne ya sa mutane da yawa suka yarda su zauna.”
“Bayan wani dan lokaci sai aka kira mutanen da suka ki zama aka ce musu idan ba su zo ba to za su rasa ayyukansu. Don haka wasu da dama iri na sai suka ji tsoro suka je.
“Kawai sai suka rufe mu muka dinga aiki, sai dan lokacin hutu gajere da suka ware mana, ba a bari mu yi salla, babu ziyartar ‘yan uwa, a haka wasun mu suka shafe wata uku a nan, akwai wani abokin aikina da yake shafe sa’a 24 yana aiki ba kakkautawa.”
Hamza ya ce ya yi farin ciki da ‘yan sanda suka ceto su daga wajen kuma ba karamar murna danginsa suka yi ba a ranar Litinin.
”Iyalaina sun yi farin ciki sosai don sun dade ba su ganni ba. Ina rokokn gwamnati da ta samar mana da ayyukan da suka fi wannan don ‘yan kasashen waje su daina zuwa suna bautar da mu irin haka,” kamar yadda ya ce.
‘Neman taimako’
Shugaban wata kungiyar kare hakkin dan adam ta Global Human Rights Network, Karibu Yahaya Kabara ne ya fara samun labarin abin da ke faruwa a kamfanin.
“Wajen karfe biyar na yamma a ranar Lahadi aka kira ni a waya na ji mutumin na kuka, yana rokona cewa mu zo mu taimake su, ya ce wani kamfani ya kulle su tsawon wata uku kuma an ki ba su damar yin sallah da zuwa ganin iyalansu da ma ba su kulawa idan ba su da lafiya.”
”Nan da nan na tambaye shi adireshin wajen daga nan sai na sanar da ‘yan sanda na kuma bi su muka je har kamfanin a jiya don kubutar da mutanen.””Abin da idona ya gani na da ban takaici. Wajen da aka ajiye ma’aikatan nan suna kwana ko dabbobi bai kamata a ajiye su a nan ba. Babu isasshen abinci, ba a biyan su sannan ba a ba su ko da magani idan ba su da lafiya,” in ji Kabara.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Kano DSP Abdullahi Haruna ya ce, ana gudanar da bincike a kan lamarin ”amma lamari ne na cin zarafin mutane” ta hanyar rufe mutane ba da son ransu ba.
“Mun je mun fitar da ma’aikatan daga wajen kuma muna ci gaba da bincike kan abin da ya faru, nan ba da dadewa ba za mu sanar da al’umma sakamakon binciken.
Wata majiyar daga ‘yan sandan da ta bukaci a sakaya ta ta fadi yadda take kallon lamarin.
”Wadannan mutanen su da kansu suka je suka nemi aiki a wajen nan sannan ba su yi korafi ba a baya, su kuma kamfanin da suka ga an shiga dokar kulle sai suka ga ba za su iya hakura da dakatar da aikinsu ba, sai suka yi amfani da halin talaucin da mutanen ke ciki suka yi musu alkawarin karin kudi idan sun ci gaba da aikin.
”Don haka babu wani kokwanto kamfanin nan sun tafka babban laifi kuma shugabannin kamfanin sun amsa laifinsu.”Manema labarai sun  tuntubi masu kula da kamfanin Kareem Saka da Mallam Hassan don jin ta bakinsu amma lambobin wayarsu ba sa tafiya kuma ba su amsa sakon da aka tura musu ba.
Tuni dai hukumomi suka rufe kamfanin sannan ana tsare da mutum biyar don bincikar su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here