An Damke Wanda Ake Zargi Da Ya Yi Wa Jaririya ‘Yar Wata 3 Fyade – Dakarun NSCDC

0
709

Daga Usman Nasidi Da Rabo Haladu

JAMI’AN hukumar NSCDC sun cafke wani matashi mai shekaru 27 da haihuwa, Ahmadu Yaro, wanda ake zarginsa da yin lalata da jaririya mai watanni uku da haihuwa a duniya a wani kauyen Adogi, dake karamar hukumar Lafia, na jihar Nasarawa.

A cikin wata guda, an yi wa kananan yara har shida fyade a kauyen na Adogi, Kamar yadda ya auku a ranar 27 ga watan Mayu, inda an yi wa wata karamar yarinya mai suna Rukayya Aliyu fyade wanda ita ma wannan jaririya ba ta wuce kwanaki 90 a Duniya ba.

Rahotanni sun bayyana cewa an yi yunkurin yin irin wannan lalata da wata jaririya mai watanni biyu da haihuwa. An kai wannan hari ne jim kadan bayan an yi lalata da Rukayya Aliyu.

An fahimci a kan yi amfani da irin wadannan kananan yara ne wadanda ba su wuce watanni uku zuwa shida da zuwa Duniya ba. Daga nan kuma a jefar da su a kusa da wata makaranta.

Ana zargin cewa masu garkuwa da mutane da ‘yan fashi da-dama su na zama a wannan kauye. Haka zalika akwai malaman tsibbu da su ka shahara a jihar da su ke zaune a garin na Adogi.

Binciken da majiyarmu ta yi, ya bayyana mata cewa akwai wasu miyagu a kauyen da ke yi wa irin wadannan mutane da su ka saba yin mummunan fyade farautar jarirai da za ayi amfani da su.

Babban jami’in NSCDC na jihar Nasarawa, Gidado Fari, ya ce za a gurfanar da Ahmadu Yaro a gaban kotu. Za a yi wannan ne da zarar an kammala binciken da ake yi a kan matashin.

Gidado Fari ya shaida wa ‘yan jarida a ranar Laraba cewa Yaro ya amsa laifinsa, tare da bayyana wa jami’an tsaro yadda ya yi wa wasu kananan yara biyar irin wannan danyen aiki.

Fari ya ce wan da ake zargin ya na ikirarin cewa ya na fama da tabin hankali, abin da ba a iya tabbatarwa ba tukuna. Ana zargin shi kadai ne ya ke addabar mutanen kauyen da fyade.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here