APC Ta Zama Barazana Ga Buhari Da Gwamnatinsa – John Oyegun

  1
  436
  Rabo Haladu Daga Kaduna
  TSOHON shugaban jam’iyyar APC mai mulki  John Odigie-Oyegun, ya ce jam’iyyar a yanzu tana matsayin “baraza ce ga Shugaba Buhari da gwamnatinsa”.
  Kafafen yaɗa labarai sun ambato Odigie-Oyegun yana wannan magana ce cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar, inda ya ce ya kamata kwamitin amintattun jam’iyyar ya kafa kwamitin riƙon ƙwarya da zai shirya taron ƙasa na musamman.
  Yayin da APC ta bayyana tsohon gwamnan Oyo, Abiola Ajimobi a matsayin shugabanta na riƙo, shi ma sakataren jam’iyyar na ƙasa Victor Giadom ya ce shi ne shugabanta.
  Hakan ya biyo bayan hukuncin da Kotun Ɗaukaka Ƙara ta yi ne na tabbatar da sauke Adams Oshiomhole daga muƙamin shugaban jam’iyyar na ƙasa.
  Wanne tasiri rikicin APC zai iya yi a kan jamiyyar?
  A cikin wata maƙala da ya yi wa taken “Before It Is Too Late” wato “Kafin a Makara”, Oyegun ya yi kira ga Buhari da kuma gwamnoni da su kawo ƙarshen abin da ya kira “abin kunya” da ke faruwa a sakatariyar jam’iyyar.
  “Jam’iyyarmu ta APC na ta yin ƙoƙarin kawo wa ayyukan gwamnatinmu da shugabanmu barazana,” in ji shi.
  Ya ƙara da cewa: “A ‘yan watannin da suka gabata, mun ga yadda jam’iyyar ta sauka daga kan aƙidu na dimokuraɗiyya, abin da ya sa duk waɗanda suka yi zaton ganin alƙawarin sauyin da ta yi musu suka zarge ta da munafurci.
  “Saboda haka wajibi ne mu riƙa tunawa cewa nasarar da muka yi a shekarar 2015 da kuma karɓar mulki cikin ruwan sanyi wani gwaji ne da ke nuna matuƙar ci gaba game da dimokuraɗiyya a ƙasarmu.”
  Cif John Odigie-Oyegun ne ya jagoranci APC a babban zaɓen 2015 da ya bai wa Shugaba Muhammadu Buhari nasarar doke shugaba mai-ci Goodluck Jonathan.
  A makon nan ne kwamitin tantance masu neman takarar gwamna na jam`iyyar APC a Jihar Edo ya tabbatar da cire Gwamna Godwin Obaseki daga cikin waɗanda za su yi takarar, abin da ya yi sanadiyyar komawarsa jam’iyyar adawa ta PDP.

  1 COMMENT

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here