Buhari Ya Ba Shugaban Rikon Kwarya Tabbacinsa.

0
320
Rabo Haladu Daga Kaduna

SHUGABA Muhammadu Buhari  ya mara wa shugaban rikon kwarya na jam’iyyar APC, Victor Giadom baya.

Ya kuma bayyana cewa zai halarci taron shugabannin jam’iyyar APC da Giadom zai gudanar ta kafar yanar gizo gobe.

Mai magana da yawun shugaban Malam Garba Shehu ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwar da ya fitar.

A cikin sanarwar Shehu ya umarci kafofin yada labarai da su daina yada labaran bogi a kan wannan batu.

Ana sa ran cewa gwamnoni da ‘yan majalisar tarayya ma zasu halarci wannan taron na gobe.


LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here