Najeriya Na Bukatar Karin Dakarun Sojoji Don Yakar ‘Yan Boko-Haram – Gwamna Zulum

0
306

Muhammad Sani Gazas Chinade, Daga Maiduguri

GWAMNAN Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya bayyana cewar, lalle Nijeriya na bukatar kara yawan dakarun tsaronta Sojoji don samun nasara a kan ‘yan ta’addar Boko Haram da ta dau tsawon lokaci tana fafatawa da su Gwamnan na Borno ya yi wannan bayani ne a lyayin da wata  tawaga daga majalisar dattijai ta kai ziyara jihar, domin yi wa al’umma jaje da ta’aziyyar
hare-haren da mayakan Boko Haram ke kaiwa a garuruwa daban-daban a jihar tabBorno.

Wannan tawagar sanatocin, na karkashin jagorancin shugaban masu rinjaye a majalisar, Sanata Yahaya Abdullahi, hadi da mai tsawatarwa, Sanata Orji Kalu, sun ziyarci birnin Maiduguri ne, don nuna alhininsu ga al’ummar jihar bisa ga yawaitar hare-haren na baya-bayan nan da ke afkuwa a yankin.
Zukum  ya shaida wa ’yan majalisun da su ka ziyarci jihar, inda a ciki har da tsohon gwamnan jihar ta Borno, Sanata Kashim Shettima, cewa
akwai karancin sojojin da su ke tunkarar wannan fafatawa, “Sannan kuma wani muhimmin abu shi ne, mu na son Gwamnatin Tarayya ta dauki
matakin shigar da hazikan matasanmu na ‘Cibilian JTF’ cikin rundunar sojojin Nijeriya tare da sauran bangarorin tsaro na kasar nan, wanda hakan
zai taimaka wajen kawo karshen ayyukan ’yan ta’addar Boko Haram.”
Har ila yau kuma, Gwamnan ya nemi ‘yan  majalisar dattawan da su duba wannan al’amarin wajen cike gibin da ake da shi a yaki da matsalar tsaro a wannan yankin da ma kasa baki daya.
A nasa jawabin, shugaban tawagar, Sanata Yahaya Abdullahi, ya ce zauren majalisar ya ce an damka wa kwamitin na su alhakin kai ziyara zuwa jihar
Borno tare da mika jajen su dangane da wannan kashe-kashen da jihar ke fuskanta a jihar.
Shugaban tawagar ‘yan majalisar ya yaba da kokarin da Gwamna Zulum “Wannan shi ne shugabanci abin koyi” wanda hakan ya taimaka wajen dawo da lamurra.
Sanata Abdullahi ya kara da cewa zauren majalisar dattijai, ta samu labari maras dadi, na hare-haren ‘yan kungiyar a yankunan Gubio da Monguno, wanda hakan ya jawo majalisar ta bukaci shugaban majalisar ya hadu da shugaban kasa domin tattauna wa kan yadda za a shawo kan matsalar tsaro.“Yayin da ko a jiya, shugaban majalisar dattijai ya gana da shugaba Buhari, kuma na tabbatar da cewa sun tattauna batun tabarbarewar tsaro a arewa maso gabas.
“kuma ina da tabbacin cewa a yan kwanakin nan wannan matsala za ta zama tarihi.” In ji shi.

Wasu daga cikin yan tawagar, akwai tsohon shugaban masu rinjaye a zauren majalisar, Sanata Ali Ndume, Sanata Abubakar Kyari hadi da yan majalisar wakilai biyu yan asalin jihar Borno a wannan tawaga.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here