Babban Alkalin Jihar Kogi, Mai Shari’a Nasiru Ajana Ya Rasu

0
358
Mustapha Imrana Abdullahi
Rahotannin da ke iske mu daga garin Abuja na cewa babban mai shari’a na Jihar Kogo a Arewacin tarayyar Nijeriya, mai Shari’a Nasiru Ajanah ya rasu a yau da safiyar Lahadi a Abuja.
Bayanan da ke Iske mu sun bayyana cewa ya rasu ne bayan ya yi fama da yar gajeruwar rashin lafiya
Marigayin dai ya fito ne daga karamar hukumar Okehi a cikin Jihar Kogi.
Mai shari’a Nasiru Ajanah ya rasu yana da shekaru 64 a duniya. In dai za a iya tunawa a satin da ya gabata ne Jihar Kogi ta rasa wani babban mai shari’a shugaban kotun daukaka kara a kotunan gargajiya mai shari’a Ibrahim Sha’aibu Atadoga.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here