Mun Yi Godiya Ga Shugaban Karamar Hukumar Dawakin Tofa-Al’umar Gwamai

  0
  422
  Mun Yi Godiya Ga Shugaban Karamar Hukumar Dawakin Tofa-Al'umar Gwamai Bayan Makaranta.
  
  Jabiru Hassan, Daga Kano.
  
  Al'umar dake zaune a unguwar bayan makaranta Gwamai, mazabar Gargari,  yankin karamar hukumar Dawakin Tofa sun yabawa majalisar karamar hukumar bisa aikin katafariyar magudadar ruwa da take yi domin dakile matsalar zaizayar kasa da unguwar ke fama da ita tun lokaci mai tsawo.
  
  Idan dai za'a iya tunawa, wannan unguwar tana fama da matsala ta zaizayar kasa wadda sanadiyyar haka gidaje da gonakin yankin suka shiga cikin barazanar lalacewa wanda kuma hakan ta sanya al'umar wannan unguwa suka yi ta kokarin ganin an kawo masu dauki walau daga gwamnatin tarayya ko jiha ko kuma karamar hukumar Dawakin Tofa.
  
  Sakamakon kokarin da wadannan al'uma suka yi, sai gashi majalisar karamar hukumar Dawakin Tofa bisa jagorancin Alhaji Ado Tambai Kwa ta himmatu wajen yin babbar magudadar ruwa domin dakile zaizayar kasa a wannan unguwar ta bayan makaranta Gwamai Wanda hakan ta sanya daukacin al'umar garin na Gwamai da kewaye suka yi jinjina ta musamman ga shugaban karamar hukumar ta Dawakin Tofa.
  
  Mai magana da yawun al'umar Gwamai bayan makaranta Malam Auwalu Bala yace ya zamo wajibi su godewa Alhaji Ado Tambai Kwa saboda ceto unguwar bayan makaranta da yayi, sannan kowa yaga yadda aikin magudadar ruwan ke tafiya batare da tsaiko ba kuma idan an kammala wannan aiki ko shakka babu al'umomin wannan unguwa  zasu sami kwanciyar hankali da kuma natsuwa idan damina ta sauka.
  
  Malam Auwalu Bala  ya kuma yi amfani da wannan dama wajen yin kira ga  ma'aikatar kula da muhalli ta jiha da ta ziyarci unguwar Gwamai bayan makaranta domin ganin halin da wannan guri me ciki domin taimakawa kokarin majalisar karamar hukumar ta Dawakin Tofa ta yadda za'a hada karfi wajen magànce wannan matsala ta zaizayar kasa a unguwar.
  
  A karshe Auwalu Bala yayi godiya ga sauran mutanen da suke ta dawainiyar ganin an sami dakile zaizayar kasa a a unguwar Gwamai bayan makaranta da wadanda suke tallafawa da kudaden gudanar da aiyukan kwamitin su da malaman da suke ta addu'ar fatan samun gudanar da wannan muhimmin aiki.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here