Al’ummar Yobe Sun Yi Na’am Da Nada Gwamna Buni Matsayin Shugaban Riko Na jam’iyyar APC

0
403

Sani Gazas Chinade, Daga Damaturu

AL’UMMAR Jihar Yobe sun yaba dangane da nada gwamna Mai Mala a matsayin shugaban kwamitin riko na Jam’iyyar APC da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar da suka hada da shugaban kasa Janar Muhammad Buhari suka yi a makon da ya gabata.
Shugaban jam’iyyar APC a Jihar ta Yobe Alhaji Adamu Chilariye a tattaunawarsa da wakilinmu ya bayyana cewar, wannan nadi da aka yiwa gwamna Mai Mala Buni a matsayin shugaban kwamitin riko na Jam’iyyar su ta APC babban alheri ne ga jam’iyyar ganin cewar, mutum ne da yasan baki da farin jam’iyyar kasancewar, ya rike matsayin babban sakataren jam’iyyar na kasa da jajircewasa ne ya sa jam’iyyar ta ginu musamman ganin cewar, mai girma shugaban kasa Muhammadu Buhari na goyon bayansa.
Alhaji Adamu Chilariye ya kara da cewar, gwamna. Mai Mala Buni mutum ne da ke da fasaha da kuma sanin ya kamata wajen tafiyar da harkokin al’umma wadda hakan ne zai ba shi damar cimma nasarar hada kan mambobin jam’iyyar daga sama har kasa musamman bisa rashin fahimtar juna da ke faruwa tsakanin juna a wasu yankunan kasar nan.
Shi ma da yake jawabi dangane da nada Mai Mala a matsayin shugaban kwamitin riko na Jam’iyyar tsohon shugaban tsohuwar jam’iyyar ANPP a Jihar Alhaji Sani Inuwa Nguru cewa ya yi , “Alal hakika nada gwaman Mai Mala a matsayin shugaban kwamitin riko na Jam’iyyar APC an yi haka bisa ga hangen nesa domin kuwa mutum ne da ya kware wajen tafiyar da lamurran Jam’iyyar.”
Ya kara da cewar, wannan nadi an yi shi dai-dai lokacin da ake bukata domin kuwa yadda lamurran jam’iyyar suka fara na bukatar nada kwararre irin gwamna Mai Mala don lalumo bakin zare sulhunta tirka-tirkar da ke akwai.
Shi kuwa Alhaji Sani Fema tsohon shugaban hukumar wasanni na Jihar ta Yobe, kuma mai bada shawara na musamman kan harkokin wasanni ga shugaban majalisar dattawa Sanata Ahmed Lawan, cikin jawabinsa dangane da wannan nadi cewa, yayi, agaskiya gwamna Mai Mala mutum ne Dan baiwa wadda ke da kwarewa akan harkokin siyasa, don haka akwai kyakkyawar fatar cewar, gwamnan zai iya tafiyar da aikin da aka sa shi na samo bakin zaren Samar da kyakkyawar alkibla ta bai daya ga ‘ya’yan jam’iyyar ba tare da nuna wariya ba.
Sani Fema ya ci gaba da cewar, a iya saninsa babu abin da Mai Mala ya sa a gaba ba tare da ya cimma nasara ba musamman duba da yadda ya rike sakataren Jam’iyyar kafin zaben shekarar canji ta 2015 har aka kai ga cin nasara da kuma zaben 2019 kawo ya zuwa samun nasarar lashe zaben gwamna na 2019.
Don haka ba makawa Mai Mala zai iya fidda kitse a wuta ta wajen samun nasarar sasanta duk eani rikicin da ya dabaibaye jam’iyyar ta APC cikin yardar Allah SWT.
Wani matashin dan siyasa kuma jigo a jam’iyyar APC daga karamar hukumar Nangere Malam Abdulrahman Nangere a tattaunwarsa da wakilinmu kan wannan batu cewa ya yi, ai wannan matsayi Na jagorantar Jam’iyyar APC da aka baiwa gwamna Mai Mala Buni tamfar an yj yanke ne akan gaba kasancewar an San zai iya ne a matsayin sa Na jajirtacce kuma wadda kabli da ba’adin siyasa da kuma jam’iyyar ta APC kasancewar da shi akan yanke mata Cibi.
Shi kuwa Alhaji Gambo mai sayar da Citta cikin kasuwar Potiskum cewa ya yi ai ba ko shakka gwamna Mai Mala zai iya fitar da kitse a wuta wajen ceto jam-iyyar daga shiga irin rudin da jam’iyyar adawa ta PDP ta yi a baya har ya kai ga faduwarta.
Don haka suna da kyakkyawar fata gareshi wajen samun nasarar dora jam’iyyar kan tudun tsira kamar yadda ake fata.
A gefe guda kuwa a duk yadda ka zaga a ciki da wajen Jihar ta Yobe babu abin da al’ummominta ke tattaunwa fiye da wannna matsayi da gwamnan Mai Mala ya samu ta yadda kowa ke furta albarkacin bakinsa tare masa addu’ar fatan alheri da cimma nasarar wannan babban nauyi da aka dora masa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here