Buhari Ya Kaddamar Da Aikin Shimfida Bututun Iskar Gas Na AKK A Yau Talata

0
251

Daga Usman Nasidi.

SHUGABAN Najeriya Muhammadu Buhari, a yau Talata zai kaddamar da aikin shimfida bututun iskar gas wanda zai fara tun daga Ajaokuta ya ratsa ta Kaduna kuma ya dire a Kano.

Ana sa ran kammala wannan aiki na shimfidar bututun mai tsawon kilomita 614 cikin watanni 12.

Wannan aiki na bututun gas mai fadin inci 40, zai rika jigilar iskar gas mai nauyin cubic feet biliyan 2.2 a duk rana.

Bututun zai taso tun daga Ajaokuta na jihar Kogi, kuma ya ratso ta birnin Abuja zuwa Neja da Kaduna sannan ya tuke a jihar Kano.

Majiyarmu ta fahimci cewa, an yi wa wannan aiki lakabi da AKK.

Shugaban sashen hulda da al’umma na kamfanin man fetur na kasa NNPC, Kennie Obateru, shi ne ya sanar da hakan a birnin Abuja.

Ya ce shugaba Buhari zai kaddamar da aikin ne daga nesa yana zaune a fadarsa ta Aso Villa a birnin Abuja, a wani yanayi da ‘yan Hausa ke kira ‘mai kama-da-wane’.

Za a kaddamar da aikin ne daga yankin Rigachukun na jihar Kaduna da kuma yankin kamfanin Ajaokuta na jihar Kogi tare a lokaci guda.

Da ya ke lissafa moriya ta fuskar tattalin arziki da za a ci da wannan aiki idan an kammala, Obateru ya ce zai haɓaka samuwar makamashi a cikin gidajen al’umma.

Haka kuma ya ce zai farfado da masana’antu musamman a yankunan Arewacin Najeriya.

Kazalika ya ce zai bunkasa samun wutar lantarki da kusa megawatts 3600, wanda hakan zai taimaka wajen farfado da kamfanonin hada sutura wanda shi kadai zai samar da ayyuka fiye da miliyan 3.

Obateru ya ci gaba da cewa, ana sa ran idan an kammala shi, wannan aiki zai taimaka wajen samar da makamashin da masana’antu ke bukata musamman na takin zamani da sauransu.

Idan ba a manta ba, a shekarar 2008 ne majalisar zartarwa ta tarayya ce ta amince da wannan aiki, inda kuma gwamnatin shugaba Buhari ta ba da kwangilarsa a shekarar 2017.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here