Dattijon Da Ake Zargi Da Yin Fyade Ya Ce Kasuwanci Ne Tsakaninsa Da Yarinyar

0
287

Daga Usman Nasidi.

WANI tsoho mai shekaru 71 da aka kama shi da laifin yi wa yarinya mai shekaru 13 fyade tare da amfani da ita wurin yin sata a jihar Gombe, ya bada labarinsa.

A yayin da aka tambayi Ashiru Sule a kan yadda abun ya faru, ya ce “yarinya ta sanar da cewa nayi mata fyade kuma na ce ta dinga sato min masara. Ni ina siyar da masara ne kuma ita ke kawo min.”

Bayan da aka tambaye shi ko yarinyar manomiya ce da har take kawo mishi masara yana siya. Sai yace shi bai san satowa take ba.

“Koda aka tambayeni dangantakar da ke tsakanina da yarinyar, nace abokiyar kasuwanci na ce. Tana kawo min masara ni kuma ina siya. Ta ce min mahaifiyarta ke aiko ta da masara don ta siyar min.

“A da ina zuwa kauyuka saro masara amma na daina saboda tana kawo min,” yace.

Ya kara da cewa, “A farkon haduwarmu, wani yaro ne yace yana sonta. Bayan kasuwanci, babu abinda ke hada mu amma an ce ina mata fyade. Hakan kuwa bai taba faruwa ba.”

A zargin da ake wa tsohon na cewa ya bata layar zana, ya yi bayanin cewa “ban san komai game da layar ba. Zan iya rantsewa da Qur’ani.”

A kan zargin fyaden da yarinyar ta ce yayi mata a kalla sau goma, tsohon ya ce zai iya rantsuwa da Qur’ani cewa bai taba lalata da ita ba.

Malam Ashiru Sule ya sanar da manema Labarai cewa yana da mata daya da kuma ‘ya’ya 12

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here