Gwamnati Ta Rika Kashe Kudaden Tsaro Kamar Yadda Ya kamata-Haruna Yusuf

1
407
Haruna Yusuf Abba,

Isah Ahmed Daga Jos

KUNGIYAR fafutukar kare hakkin al’umma da cigaban  siyasa ta matasan  Najeriya, ta bukaci gwamnatin tarayya da gwamnatocin  jihohi, da kananan hukumomi, su rika kashe makudan kudaden da suke warewa harkokin tsaro, a wuraren da suka kamata. Kungiyar ta bayyana wannan bukata ce, a wajen wani taron ‘yan jarida da ta kira a garin Jos, kan matsalar tsaron da ake fama da shi, a yakin arewacin Najeriya.

Da yake yiwa ‘yan jarida jawabi a wajen taron, shugaban kungiyar Haruna Yusuf Abba ya bayyana cewa abin takaici ne ganin irin makudan kudaden al’ummar Najeriya da gwamnatocin tarayya da gwamnatocin jihohi da kananan hukumomi, suke warewa da sunan tsaro, amma ba a amfani da su a wuraren da suka kamata.

Ya ce a kullum wadannan  gwamnatoci suna  kashe makudan kudade  da sunan tsaro, amma matsalar tsaron sai dada lalacewa take yi, musamman a yankin arewacin kasar nan.  Saboda ba a amfani da wadannan kudade a wuraren da suka kamata.

Har’ila yau ya yi  kira ga shugaban kasa da gwamnan jihar Filato a  su   tashi tsaye don ganin an magance matsalar tsaron da ke damun yankin arewa.

‘’Muna kira ga gwamnan Filato a matsayinsa na shugaban gwamnonin arewa,  ya kira gwamnonin arewa su shirya yadda zasu magance matsalolin da suke faruwa a arewa,  na rashin tsaro da talauci. Haka kuma  muna kira ga shugaban kasa,  ya zakulo wadanda suke kashe-kashe a arewa,  domin a hukumta su’’.

Ya yi   kira ga sojoji da ‘yan sanda su tsaya tsayin daka wajen gudanar da ayyukansu,  na tsaro don ganin an magance matsalar tsaron da ake fuskanta a kasar nan.

Daga nan  ya yi kira ga hukumomin yaki da almundahanar kudade na kasar, na  EFCC da ICPC su ci gaba da kwato  kudaden  al’ummar kasar nan, da wasu shugabannin kasar nan suka sace.

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here