Makarantun Yara Da Makarantun Firmare Za Su Ci Gaba Da Zama A Rufe – FG

0
359

Daga Usman Nasidi.

GWAMNATIN tarayya ta ce za a ci gaba da rufe makarantun kananan yara da makarantun firamare da ke fadin kasar nan.

A sanarwar da ta fito kafin wannan, gwamnatin tarayya ta ce za a bude makarantu daga matakin firamare zuwa sakandire domin bawa daliban da ke shekarar karshe damar rubuta jarrabawa.

Sai dai, a cikin wata sanarwa da Dakta Sani Aliyu, jagoran kwamitin yaki da annobar korona a kasa, ya fitar a Abuja ya ce ba za a bude makarantun kananan yara da makarantun firamare ba.

“Ba za a bude makarantun kananan yara da makarantun firamare ba har sai sanarwa ta gaba ,” a cewarsa.

A baya majiyarmu ta samu labarin cewa gwamnatin tarayya ta amince da bude makarantu a fadin kasar nan.

Hakan ya biyo bayan taron da ya wakana tsakanin kwamitin yaki da cutar korona na fadar shugaban kasa (PTF) da shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Kamar yadda gwamnatin tarayyar ta bayyana, azuzuwan da za su koma bakin karatun sun hada da:
1. Aji shida na dukkan makarantun firamare.
2. Daliban aji uku da na aji shida na makarantun sakandaren da ke fadin kasar nan.

Hakazalika, gwamnatin tarayyar ta amince da bude shige da fice tsakanin jihohin kasar nan, amma matukar ba a zarta lokutan doka ba.

Gwamnatin tarayyar ta kara da amincewa da sauka ta tashin jiragen sama a cikin fadin kasar nan kadai.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here