Matakin Da Buhari Ya Dauka Kan APC Ya Yi Daidai-Pasali

0
406
Alhaji Danladi Garba Pasali

Isah Ahmed Daga  Jos

 SHUGABAN kungiyar yakin neman zaben shugaban kasa Muhammad Buhari, ta Buhari Campaign Organization [BCO] Alhaji Danladi Garba Pasali ya bayyana cewa matakin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dauka, na rushe shugabannin jam’iyyar APC na kasa, tare da kafa kwamitin riqo kasa, ya yi dai dai. Alhaji Danladi Garba Pasali ya bayyana haka ne, a lokacin da yake zantawa da wakilinmu.

Ya ce dole ne jam’iyya mai karfi da mai mulki kamar APC, ta zamanto akwai shugabanci na jam’iyya,  akwai  kuma shugabanci na shugaban kasa.

Ya ce  idan aka dubi sauran jam’iyyu na baya, akwai kwamitun amintattu na jam’iyya. Amma sai aka sami  kuskure a jam’iyyar APC tun da farko,   aka ki a kaddamar da kwamitun amintattu na jam’iyyar, saboda shiritar da shugabannin jam’iyyar suke ta yi,  suka mayar da jam’iyyar kullum sai hada fitina, saboda babu masu tsawatar masu.

‘’Don haka fitowar da shugaban kasa  ya yi ya tsawatar, kuma ya sanya wannan jam’iyya a  hanya, ta hanyar rushe shugabannin jam’iyyar, tare da kafa kwamitin riko ya yi dai dai.

Domin bai kamata abar abubuwa su cigaba da lalacewa a  jam’iyyar ba,   ta zama babu biyayya,  shugaban jam’iyyar bai san mahimmancin ‘yayan jam’iyyar  ba. Idan kana da damuwa a  jam’iyyar, babu wanda zaka kaiwa kuka’’.

Alhaji Danladi Pasali ya yi bayanin cewa  kwamitin rikon nan da shugaban kasa ya kafa, babu shakka an samo dattawa masu mutumci da sanin ya kamata, da zasu kawo gyara a  jam’iyyar.

Ya ce tun daga lokacin da shugaban kasa ya  dauki wannan mataki,  dukkan  magoya bayan  jam’iyyar  sun yi murna,  saboda basa  jin dadin abubuwan da suke faruwa a   jam’iyyar.

Ya yi  kira ga dukkan magoya bayan  jam’iyyar, su baiwa kwamitin riko  goyan baya da hadin kai,  domin ya  sami nasarar  gyara   jam’iyyar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here