Usman Dangwari Ya Shawarci Gwamnatin Tarayya Kan Sake Sa Dokar Zaman Gida.

0
338

Alhaji Usman Dangwari.

 Jabiru Hassan, Daga Kano.

Wani  dan kasuwa kuma mai sharhi kan al' amuran yau da kullum dake kano Alhaji Usman Dangwari ya shawarci gwamnatin tarayya data  duba batun sake rufe wasu jihohin kasarnan kan annobar Covid-19  duba da yadda aka fuskanci kunchin rayuwa lokacin da aka yi rufewar farko.

Yayi wannan kira ne a ganawarsu da wakilin mu tareda bayyana cewa yana dakyau ayi waiwaye kan irin matsaloli da wahalar da al'umar kasar nan suka fuskanta lokacin da aka garkame kasar  da  farko musamman yadda aka yi asarar rayuka da dukiyoyi wanda kuma hakan ya jawo koma baya wajen ci gaban tattalin arziki da cinikayya.

Alhaji Usman Dangwari ya kuma nunar da cewa akwai bukatar ganin gwamnatin tarayya tayi wani kyakkyawan tanadi musamman ga talakawan Nijeriya kafin ta sake rufe kasa ta yadda al'uma zasu zauna a gudajensu suna da abin da zasu ci sabanin yadda aka yi a rufewar farko wadda aka fuskanci wahalhalu na rashin abin da za'a ci da rashin magunguna da sauran muhimman abubuwa na rayuwa.

Yace yanzu lokaci ne na damina, kuma wannan gwamnatin ta shugaba Muhammadu Buhari tana da kyawawan manufofi kan sha'anin noma, sannan manoma sun amsa kira sun kama aiki sosai Wanda kuma idan aka sake sanya dokar zama a gida ko shakka babu za'a yi asarar abin da aka shuka kuma daga karshe a samu karancin kayan amfanin  gona sanadiyyar hana fita.

A karshe dan kasuwar ya nunar da cewa Allah ya baiwa Nijeriya arziki mai tarin yawa, amma abin takaici shine  idan ma gwamnati ta bada abu a baiwa yan kasa baya isa garesu  sai da danne  saboda masu son ci gaban kasar basu da yawa saboda son zuciya da hadamar abin duniya

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here