Yadda Aka Yi Wa Yarinya Fyade Aka Jefar Da Gawarta A Masallaci A Kaduna

0
349
Rabo Haladu Daga Kaduna
HUKUMOMI a jihar Kaduna  sun tabbatar da cewa yarinyar nan da aka ga gawarta a wani masallaci a makon jiya fyade ne aka yi mata.
Kwamishinar kula da harkokin mata da walwalar jama’a ta jihar ta shaida manema labarai  cewa rahoton binciken da ta samu ya nuna cewa fyade ne aka yi mata kuma ta ce yanzu haka jami’an tsaro sun dukufa don gano wanda ya yi mata fyaden.
A ranar Juma’a ne aka tsinci gawar yarinyar a wani masallaci da ke unguwar Kurmin Mashi, lamarin da ya tayar da hankalin jama’a da dama.
Bayanan da mañema labarai  suka samu sun ce lamarin ya afku ne a unguwar Kurmin Mashi da ke yankin karamar hukumar Kaduna Ta Kudu.
Wani Mazaunin unguwar ne ya fara ganin gawar yarinyar yashe a cikin masallacin inda nan take mutane suka taru suna nuna takaicinsu da kuma mamaki.
Bayan da ‘yan sanda suka isa wurin ne sai aka nemi iyayenta. Malam Yau Abdullahi shi ne mahaifin yarinyar ‘yar shekara shida.
”Tana cikin gida tana wasa ba a ankara ba sai aka ga ba ta nan. Na dawo daga masallaci sai aka ce min ba a ganta ba. To wallahi har yanzu ba mu san yaya aka yi ta bace daga cikin sauran yara da suke wasa tsakanin cikin gida da kofar gida ba.
Tuni dai gwamnatin jihar Kaduna ta ce ta kaddamar da bincike don gano wanda ya aikata fyaden. Hajiya Hafsat Baba ita ce kwamishinar kula da jin dadin jama’a ta jihar, ta kuma za su gabatar da rahoton bincikensu ga gwamna.
”Har yanzu ba a kai ga kama kowa ba amma jami;an tsaro suna kokarinsu sosai.
”Al’amarin nan na ba mu tsoro don lamarin fyade karuwa yake yi a Kaduna kowace yara.”
Haka ma Manama labarai  sunji  ta bakin daya daga cikin mutanen da suka yi uwa suka yi makarbiya wajen ganin an kai gawar yarinyar asibiti don gudanar da bincike.
Farfesa Hauwa Yusuf mamba ce a kungiyar yaki da cin zarafin al’umma da mata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here