Lalong Ya Umarci A Yi Wa Dukkan Kwamishinonin Filato Gwajin Cutar Koruna

0
345

Isah Ahmed Daga Jos

GWAMNAN Jihar Filato Simon Lalong ya   umarci a yi wa  dukkan kwamishinoni  da  ‘yan majalisar zartarwa  jihar,  gwajin cutar annobar Koruna  tare da killace kan su. Sakamakon kamuwa da cutar da  kwamishinan ciniki da masana’antu na  jihar, Mista  Abe Aku ya yi. Gwamnan ya bada wannan umarnin ne, a yammacin ranar larabar nan a garin Jos. Wata sanarwa da ke dauke da sanya hanun kwamishinan watsa labaran jihar, Mista Dan Manjang da aka raba wa ‘yan jarida ce ta bayyana haka.

Sanarwar ta ce sakamakon wannan umarni da gwamnan ya bayar, za a dauki gwajin kwamishinonin tare da sauran ‘yan majalisar gudanarwar jihar, a tura zuwa cibiyar binciken cututtuka ta kasa da ke Vom.

Sanarwar ta shawarci jama’a su guji ziyartar kwamishinonin da ‘yan majalisar zartarwar, a yayin da suka killace kansu.

Idan ba a manta ba  a kwanakin baya ne gwamnan da iyalansa aka yi masu gwajin wannan cuta, kuma sakamakon gwajin da ya fito ya tabbatar basu xauke da wannan cuta.

A wata sabuwa kuma kwamishinan lafiya na jihar  Dokta Nimkong Lar ya bayyana cewa mutane 8 ne, suka rasa rayukansu sakamakon kamuwa da wannan cuta a jihar Filato. A yayinda mutane 4 masu dauke da wannan cuta, suka tsere  daga wajen ake yi masu jinya.

Har’ila yau ya ce ya zuwa yanzu mutum 330 ne suka kamu da wannan cuta, a Jihar Filato. A cikin wadannan mutane da suka kamu da wannan cuta mutum 41 ma’aikatan kiwon lafiya ne.

Ya ce mutum 156 masu dauke da wannan cuta a jihar  ne suka warke kuma tuni an sallamesu sun koma cikin iyalansu.

Ya ce mutum 4076 ne aka yiwa gwajin wannan cuta a jihar kuma an sami sakamakon mutum3471. Yanzu ana jiran sakamakon mutum 605.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here