COVID-19: Almajirai 193 Sun Kamu Da Cutar Korona A Kano

0
341

Daga Usman Nasidi.

GWAMNATIN Jihar Kano ta ce a kalla almajirai guda 193 ne suka kamu da cutar COVID-19 da aka fi sani da coronavirus a jihar.

Kwamishinan Ilimi na Jihar, Sanusi Muhammad Kiru, yayin jawabin da ya yi wa manema labarai a ranar Alhamis ya ce kawo yanzu Kano ta mayar da almajirai 1,500 zuwa jihohinsu na asali.
Ya kuma ce an dawo wa jihar Kano almajirai 4,000.

Har wa yau, ya ce jihar ta haramta makarantun allo, ya ce duk wanda ke son kafa makarantar allo sai ya samar wa daliban dakin kwana.

“Ba za mu amince da yadda Alaramomi ku kwaso dalibai kimanin dubu daya ba amma ba su da wurin da za su ajiye su,” in ji shi.

Shugaban kwamitin yaki da COVID-19 na jihar, Dakta Tijjani Hussain ya ce cikin samfurin mutum 2000 da suka karba yayin bi gida gida a karamar hukumar Nasarawa, mutum daya ne kawai ke dauke da cutar.

Wannan ya ci karo da abinda Hukumar NCDC ta fitar na cewa karamar hukumar Nasarawa tana daya daga cikin kananan hukumomi da cutar ta yiwa katutu.

Hussain ya kuma nuna damuwarsa a kan halin da wasu mutane a jihar ke nunawa, ya ce wasu har yanzu ba su saka takunkumin fuska saboda ba su yarda akwai cutar ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here