Ganduje Ya Cire Dokar Kulle A Kano

0
278
Rabo Haladu Daga Kaduna
GWAMNAN Kano Abdullahi Umar Ganduje ya janye dokar kulle da ke aiki a jihar.
Ma’aikatar lafiya ta jihar ce ta sanar da hakan a shafinta na Twitter ranar Alhamis.
Gwamnatin ta ce ma’aikata daga mataki na 12 zuwa sama za su koma aiki daga ranar Litinin 6 ga watan Yuli.
Sannan ana ci gaba da tattaunawa kan ranar da za a bude makarantu ga dalibai da ke shekarar karshe da masu rubuta jarrabawar kammala aji uku da ‘yan firamare masu rubuta jarabawar shiga sakandare.
Hakazalika cire wannan doka na nuni da cewar an bude dukkan wuraren da aka kulle a baya amma dole su tabbatar da matakan kariya a wuraren harkokinsu kamar yadda hukumomin lafiya suka umarta, a cewar kwamishinan yada labarai na Kano Malam Muhammad Garba

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here