Gwamna Masari Ya Shirya Taron Addu’a Na Musamman

0
328

Daga Usman Nasidi.

GWAMNAN jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya shirya taron addu’a na musamman kan harkokin yan bindigam garkuwa da mutane da satar shanu da ya addabi al’ummar jihar shekarun nan.

A ranar Alhamis, 2 ga Yuli aka kaddamar da wannan taron addu’ar kuma za’a kwashe kwanaki uku ana yi, kamar yadda majiyarmu ta samu labari.

An fara na yau ne misalin karfe 10 na safe a Masallacin Juma’ar dake birnin jihar inda mahaddata Al-Kur’ani sama da 300 suke sauka.
An kwashe awanni uku a saukar yau.

A cewar masu ruwa da tsaki, an kaddamar da taron addu’ar ne bisa bukatar al’ummar jihar domin shawo kan lamarin rashin tsaron da ya addabi jihar.

Hakazalika an yi hakan ne domin nunawa jami’an tsaron dake faggen fama cewa al’ummar na nasu iyakan kokarin wajen ganin an kawar da yan binsigan.

Daga cikin wadanda suka halarci taron sune mataimakin gwamnan jihar, Injiniya MannirYakubu; kwamishanan labarai, Alhaji Abdulkareem sirika; mai baiwa gwamna shawara kan tsaro, Ibrahim Ahmad da sakataren din-din-din ma’aikatar harkokin addini, Mohammad Lawal Mua’zu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here