Matan Aure Da Masu Aiki Nake Yi Wa Fyade – Dan Fashi Da Makami

0
398

Daga Usman Nasidi.

A RANAR Laraba, 1 ga watan Yulin 2020, dan fashi da makami mai suna Adeniyi Ajayi, ya bayyana cewa matan aure da ‘yan aiki yake wa fyade a kan idon mazansu don hakan ya zama ladabtarwa idan aka hana shi kudi yayin da yaje fashi da makami.

Rahotanni sun bayyana cewa Adeniyi ya shiga hannun jami’an runduna ta musamman ta yaki da fashi da makami ta jihar Legas.

Sun kama shi a wani otel da ke yankin Ijora 7-up a jihar.

Adeniyi wanda ke fashi da makaminsa shi kadai, ya addabi jama’ar Sabo, Ijora Badia da sauransu. A lokacin da aka bayyana cewa an kama shi, mata takwas wadanda suka hada da ma’aikatan gwamnati da lauyoyi sun isa ofishin SARS don tabbatar da cewa ya yi musu fyade bayan fashi da makami da yayi.

‘Yan mata biyu da ke aiki a wani kamfani a Sabo, sun ziyarci ofishin SARS inda suka bayyana yadda wanda ake zargin ya yi musu fyade a gaban abokan aikinsu maza, da rana tsaka a ranar 16 ga watan Yunin 2020.

Sun ce ya kwace musu wayoyi, kwamfuta biyu da ATM a yayin fashin.

A yayin zantawa da manema labarai, wanda ake zargin ya roki ‘yan sandan da su kashe shi a maimakon mika shi gidan gyaran hali.

Kamar yadda yace, zai sake kekashewa a matsayin dan ta’adda idan aka kai shi gidan yari.

“Tun watan Janairun 2019 nake wannan aikin da tocila. A yayin aikin, na kan bai wa sauran runduna ta umarni duk da ni kadai ne don tsoratar da wadanda nake wa fashin.

“Ina yi wa mata fyade a gaban mazansu idan basu bani kudi ba don hukunta mazan. Ina yi wa masu aiki fyade. Ina amfani da kudin wajen biyan kudin otal.

“Hanya daya da za a shawo kan wannan matsalar shi ne salwantar da rayuwata. Idan aka tura ni gidan yari zan sake kekashewa ne. Bana son in ci gaba da damun ‘yan Najeriya,” yace.

Ya kara da cewa, “Lokacin farko da aka kama ni an kaini gidan gyaran hali saboda sata da nayi. Sauran abokaina a can sun dinga zundena saboda karamin laifi ya kaini. Sun ce in shiga kungiyarsu idan mun fita. Saboda haka na ce gara a salwantar da rayuwata da dai a kaini gidan yari.”

A lokacin da aka tambayesa meye salwantar da rayuwarsa, ya ce a kasheshi kawai don babu wanda ya damu da shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here