‘Yan Fashin Teku Sun Kama ‘Yan Najeriya 9

0
269

Rabo Haladu Daga Kaduna

WASU ‘yan fashin teku sun kai wa wani jirgin ruwan dakon mai da tace shi daura da gabar Najeriya, tare da kama wasu ‘yan Najeriyar 9.

Ana wa Jirgin ruwan na Sendje Berge wasu gyare-gyare ne a lokacin da aka kai harin a cewar wani babban jami’i na kamfanin BW Offshore mai mallakar jirgin ruwan.

Kamfanin mai hedikwata a Oslo ya ce babu wani daga cikin sauran mutanen da ke cikin jirgin ruwan da ya samu rauni.

“Muna aiki yanzu da hukumomin Najeriya domin ceto ‘yan Najeriyar nan da aka yi awon gaba da,” a cewar Andreassen.

Jirgin, wanda ke tace danyen mai da kuma adana shi duk a bisa ruwan, wanda kuma ke iya samar da gangar mai 50,000 a kullun, na aiki ne a rijiyoyin mai na Okwori, da kamfanin man Addax, reshen babban kamfanin Sinopec na China, ke gudanarwa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here