Gwamnan Bauchi Ya Dakatar Da Sarkin Misau Alhaji Ahmed Sulaiman

0
460
Gwamnan Al'umma Bala Muhammad

Rahoton Z A Sada

GWAMNAN jihar Bauchi, Bala Muhammad Kaura, ya dakatar da Sarkin Misau, Alhaji Ahmed Sulaiman sakamakon tashin hankali da aka samu a yankin tsakanin manoma da makiyaya.

Tashin hankalin a wannan mako, a garin Zadawa da ke cikin karamar hukumar ta Misau, ya yi sanadiyyar mutuwar akalla mutum tara da jikkata wasu da dama.

Gwamna Bala Kaura ya sanar da dakatar da Sarkin ne yayin ƙaddamar da wani kwamiti da zai gudanar da bincike kan rikici mai nasaba da wani fili da ake takaddama a kai.

Gwamnan na jihar Bauchi ya kuma dakatar da wasu sarakunan gargajiya masu mukaman hakimi da dagaci a yankin da rikicin ya shafa.

Sarkin Misau dai na daga cikin manyan sarakunan gargajiya a jihar ta Bauchi.

Tun farko Gwamnan ya dakatar da shugaban riko na karamar hukumar ta Misau da wasu manyan jami’an karamar hukumar. Gwamnatin jihar na zarginsu da yin sakaci game da rikicin.

Gwamnan ya ce an dakatar da jami’an da sarakunan gargajiyar ne domin bayar da damar gudanar da bincike. Dakatarwar za ta ci gaba da aiki zuwa lokacin da za a kammala bincike.

Short presentational grey line
A 2015 ne dai aka nada Alhaji Ahmad Sulaiman Sarkin MisauHakkin mallakar hotoTWITTER/@MASARAUTARMISAU
Image captionA 2015 ne dai aka nada Alhaji Ahmad Sulaiman Sarkin Misau
Short presentational grey line

An ba kwamitin binciken da aka kaddamar makwanni uku ya gabatar da rahotonsa. Kawo yanzu ba a kai ga jin ta bakin shuwagabannin da aka dakatar ba.

A 2015 ne dai aka nada Alhaji Ahmad Sulaiman Sarkin Misau, bayan rasuwar Sarki Muhammadu Manga.

Ba a cika samun rikici tsakanin manoma da makiyaya a jihar ta Bauchi ba idan aka kwatanta da wasu jihohin Najeriya masu fama da irin wannan rikici da ma matsalar ‘yan bidiga

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here