Albashina Na Jami’ar Madina Ya Fi Wanda Ake Ba Ni A Matsayin Minista – Pantami

0
820

Daga Usman Nasidi.

MINISTAN Sadarwa, Isa Pantami ya ce albashinsa da allawus a matsayin minista bai kai abin da yake samu ba a lokacin da yake aiki a matsayin malami a Jami’ar Kasa da Kasa ta Madina a kasar Saudiyya.

Pantami ya furta wannan ne yayin da ya ke martani a kan rahotonin da wasu jaridun intanet suka wallafa na cewa ya siya manyan gidaje uku a cikin shekara guda tun bayan zamansa minista.

A cewar sanarwar da mai magana da yawunsa, Uwa Suleiman ya fitar a ranar Juma’a, ministan ya ce ya dawo Najeriya ne don “amsa kiran da aka yi masa na neman ya zo ya yi wa kasarsa hidima.”

Wani sashi daga cikin sanarwar ta ce, “Domin kawar da shakku daga zukutan mutane, Honarabul Minista bai taba siyan ko da gida daya ba a ko ina a duniya tun lokacin da ya kama aiki a matsayin minista.

“Daya daga cikin gidajen da aka wallafa, gidansa ne da yake ciki tun Janairun 2017, fiye da shekara biyu kafin ya zama minista yayin da daya kuma gidan haya ne da ya karba ranar 17 Disamban 2019. Sauran hotunan gidajen biyu kuma bai san inda aka samo su ba.

“Yana da kyau a sani cewa albashi da allawus dinsa a matsayin minista ba su kai abin da yake samu ba a lokacin da yake aiki a matsayin Farfesa a Jami’ar Kasa da Kasa ta Madina a Saudiyya, inda shi ne dan Najeriya na farko da ya fara koyarwa a wannan matsayin.

“Ya dawo gida Najeriya ne kawai saboda kishin kasa da sha’awar ganin ya bayar da gudunmuwarsa wurin ci gaban kasa.

“Dakta Pantami yana daga cikin tsirarun ‘yan Najeriya da abin duniya ba ya tsole musu ido sai dai kishin kasa da son yi wa al’umma hidima kamar yadda za a iya gani a lokacin da ya amsa kirar da aka yi masa na zuwa ya yi wa kasarsa aiki.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here