An Kashe Mana Mutane 99 A Kudancin Kaduna – Fulani Makiyaya

0
397

Usman Nasidi, Daga Kaduna.

SHUGABANNIN al’ummar Fulani mazauna kudancin Kaduna, karkashin jagorancin gamayyar kungiyoyin Fulani Makiyaya, sun bayyana cewa an hallaka musu akalla rayuka chasa’in da tara.

Sun bayyana cewa an kashe musu wannan adadin mutanen ne a watan Yuni a karamar hukumar Zangon Kataf da Kaura.

Sun kara da cewa wasu matasan kabilar Atyap da Tsam dake Zangon Kataf da Kaura ne suka aikata wadannan aika-aikan na kashesu, sace musu dukiya, da lalata musu muhalli.

Wakilin gamayyar Fulanin wanda ya yi hira da manema labarai a Kaduna ranar Juma’a ya zargi kungiyar al’ummar mutan kudancin Kaduna SOKAPU da hannu cikin kisan jama’ar Fulani.

Sakataren kungiyar Mobgal Fulbe, Nuhu Ibrahim, ya ce bayan Fulani 139 da aka nema aka rasa, an gona musu gidaje.

Amma kungiyar SOKAPU ta ce ba ta da masaniya game da kisan Fulani makiyaya 99 a kudancin Kaduna.

Kakakin kungiyar SOKAPU, Luka Binniyat, ya bayyanawa jaridar Punch cewa, ” A saninmu babu abin da ya faru a Zangon-Kataf. Ba mu da masaniya game da wani harin da aka kai wa Fulani a kauyukan Atyap.”

Duk yunkurin da aka yi na ji daga bakin kakakin hukumar yan sandan jihar, Mohammed Jalinge, ya ci tura.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here