An Yi Wa Wani Jirgin UN Ruwan Harsashi A Borno

0
423

Daga Usman Nasidi.

AN bude wa wani jirgi mai saukan ungulu mallakar Majalisar Dinkin Duniya (UNHAS) wuta a Damasak, a karamar hukumar Mobbar da ke arewacin jihar Borno.

Duk da haka, jirgin ya lallaba ya dawo sansaninsa a Maiduguri jim kadan bayan harin da aka kai masa a ranar Alhamis 2 ga watan Yulin 2020.

UNHAS na taimakawa ne wurin rabon abinci da karkashin shirin samar da abinci na duniya a yankin.

Rohotanni sun bayyana cewa an kai hari a jihar Borno, kwana guda bayan Gwamnan jihar, Babagana Zulum ya jogoranci wata tawaga zuwa Damasak don raba wa fiye da gidaje 12,000 tallafin abinci.

A halin yanzu dai ba a tabbatar idan kungiyar ta’adanci ta (ISWAP) ce ta kai wa matafiya da ke cikin jirgin harin ba.

ISWAP ta amsa cewa ita ce ta kai harin na Damasak a tashan Amaq da ta saba amfani da shi wurin wallafa ayyukan ta tare da kira ga mutane su shiga su tallafa mata.

Majiyarmu ta gano cewar jirgin, UNHAS, da aka kai wa harin fari ne da tambarin UN a jikinsa kuma samfurin Bell 412 da 212 ne da aka tura yankin domin ayyukan jin kai.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here