Ba Wanda Ya Isa Ya Hana Almajiranci – Sheikh Dahiru Bauchi

0
346

Usman Nasidi, Daga Kaduna.

SHAHARARREN shehin Malami, Fadilatus-Shiekh Dahiru Usman Bauchi, ya bayyana rashin amincewarsa da Gwamnonin Arewa bisa kokarin hana almajiranci da suke yi.

Sheikh Dahiru a hirarsa da manena labarai ya bayyana cewa ana kokarin take wa mutanen da suka yi imani da shirin almajiranci hakkinsu kuma yana daya daga ciki.

Shehi ya ce kundin tsarin mulkin Najeriya ta bai wa kowane dan kasa damar zuwa inda ya ga dama domin yin addinin da ya ga dama.

Ya ce: “Kundin tsarin mulkin kasa ta ba mu ‘yancin yin addininmu duk yadda muka ga dama. Abin da muka fi girmamawa a addini shi ne Alkur’ani.”

“Tun da addini ta ba su dokokin da za’a bi amma suka ki biyayya, shin wani hakki suke da shi na baiwa Alkur’ani umurni? saboda haka, ba zamu yarda da haramta Almajiranci da gwamnonin Arewa sukayi ba.”

“An take mana hakkin yancin yin addininmu. Ba zamu amince a take mana hakkin zuwa kowani waje a kasar nan domin aiwatar da addininmu ba.”

“Dalilin shi ne akwai gwamnati, kuma gwamnati na biyayya ne ga kundin tsarin mulki . Kundin mulkin tarayyar Najeriya ta baiwa ko wani dan kasa daman zuwa duk inda yaga daman yin addininsa. Almajirai yan Najeriya ne.”

“Kwashe mana mutane tamkar dabbobi da kaisu wurare daban-daban da ake yi, ba zamu amince ba. A matsayinmu na yan Najeriya, muna da hakkin yin addinimu. Alkur’ani ce abin farko a addinmu.”

“Ba zamu amince a hana almajiranci ba. Muna da hakkin zuwa ko ina a duniya domin karanta Alkur’ani.”

Sheikh Dahiru Bauchi ya kara da cewa gwamnonin basu nemi shawarasa ba kafin haramta Almajirancin.

Za ku tuna cewa kungiyar gwamnonin Arewa karkashin jagorancin gwamnan jihar Plateau, Simon Lalong, ta yanke shawarar mayar da Almajirai jihohinsu na asali tare da haramta almajirancin gaba daya a Arewacin Najeriya.

Gwamnonin irin na Kano, Kaduna, Nasarawa, da Neja tuni sun alanta haramcin Almajirancin a jihohinsu.

A jihar Kano, akalla Almajirai 193 ne suka kamu da cutar COVID-19. Hakazalika a jihar Kaduna da Abuja an samu da dama dauke da cutar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here