Isah Ahmed Daga Jos
KUNGIYAR masu shirya fina-finan Hausa ta Kanywood, reshen Jihar Filato ta karramar fitatcen malamin addinin musuluncin nan, da ke zaune a garin Jos, kuma daraktan ilmi na Kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa’ikamatis Sunnah ta kasa reshen Jihar Filato, Ustaz Abubakar Imam Bala Gana. Kan gudunmawar da yake bayarwa kan zaman lafiya, ta hanyar wa’azuzzukan da yake gabatarwa, a gidajen rediyo da tilbajin na Jihar Filato. Kungiyar ta karramar malamin ne, a karshen makon da ya gabata a garin Jos.
Da yake jawabi a wajen taron, Sakataren kungiyar Attahiru Babayo ya bayyana cewa sun karramar malamin ne, kan irin gudunmawar da yake bayarwa kan zaman lafiya, ta hanyar wa’azuzzukan da kake gabatarwa a gidajen rediyo da talbajin da ke Jihar Filato.
Ya ce babu shakka jama’a suna matukar amfana da wa’zuzzukan da malamin yake gabatarwa. Don haka kungiyar ta zavo shi, ta qarrama shi, don ta dada karfafa masa gwiwa kan wannan aiki da ya sanya a gaba.
‘’Daga yanzu zamu rika tuntubar Malam kan duk abin da ya shafi addinin musulunci, da zamu sanya a cikin fina finanan da muke shiryawa, domin ka rika taimaka mana’’.
Attahiru Babayo ya yi bayanin cewa kungiyar tana tallafawa al’umma, don haka a lokacin da aka yi dokar kulle na annobar Kurona a Jihar Filato, ta tallafawa mabuqa da kayayyakin abinci.
Har’ila yau ya ce a lokacin da aka aka yi rikici a Barikin Ladi a shekarun baya, kungiyar ta tallafawa wadanda rikicin ya shafa mutum 15, ta hanyar koya masu sana’ar daukar hoto.
A nasa jawabin Ustaz Abubakar Imam Bala Gana ya bayyana matuqar farin cikinsa da wannan karramawa, da aka yi masa.
Ya ce babu shakka wannan karrama zata dada karfafa masa gwiwa, kan aikin da’awar da yake gudanarwa.
Ustaz Abubakar Gana ya yi bayanin cewa addinin musulunci bai hana sana’ar fim ba. Abin da aka hana yi a fim, a addinin musulunci, shi ne a kwakwayi Allah ko Manzon Allah SAW.
‘’Akwai wadanda suke bata maku suna a wannan sana’a. kuma nasan ku kanku, bakwa jin dadin irin abin da wawannan mutane suke yi. A kowace sana’a ana samun bata gari, don haka bai kamata mutum yace gabaki daya, fim babu kyau ba. Domin Fim sana’a ce da mutane suke yi, suna samun abin da zasu rike kansu da iyalansu’’.
Ita dai tawagar wannan qungiya da suka halarci wannan taro, sun hada da uban kungiyar Alhaji Abdu Kano wanda aka fi sani da Karkuzu da shugaban kungiyar Hamza Abubakar Talle Maifata da Alhaji Tanimu Akawu da Auwal Hassan Tubarkalla da Nasiru Aliyu da Anas Hassan Tubarkalla Maihula da Tijani Lawandi Datti da Mansur Muhammad da Rabi’u Yakubu Kwande da Hajiya Fati Abubakar da Zulaiha Ishak da kuma Nafisa Abubakar.