Na Kama Matata A Ƙarƙashin Gadon Kwartonta Tsirara – Miji Ya Faɗa Wa Kotu

0
832

Daga Usman Nasidi.

WANI mutum mai suna Olalekan ya bukaci kotun gargajiya da ke Ojo Oba/Mapo ta raba aurensa da matarsa, Anudetan domin ya dena ƙaunar ta.

A cewar magi da nci yana son a raba auren su ne saboda halin rashin sanin ya kamata da rashin kulawa da ta ke da shi.

Ya ƙara da cewa tana bin maza kuma ta gudu ta bar shi da ƴarsu na tsawon shekara hudu.

Olalekan ya kuma roki kotun ta bashi daman rike ƴarsu mai shekara biyar da watanni shida.

Anudetan ta amince da bukatar raba auren da mijinta ya gabatar wa kotu inda ta ce ba ta taɓa samun natsuwa ba a auren.

Ta kuma amince a bar wa tsohon mijinta ƴarsu amma a bata damar ganinta duk lokacin da ta buƙata.

Shugaban Kotun, Cif Ademola Odunade bayan sauraron bangarorin biyu ya yanke hukuncin raba auren inda yace bisa dukkan alamu bangarorin biyu ba su son auren.

Odunade ya haramta wa wacce aka yi kara zuwa gidan wanda ya yi karar inda ya ce duk lokacin da ta ke son ganin ɗiyarta sai su haɗu a kotu.

Tunda farko, Olalekan ya shaida wa kotu cewa, “roƙon da nake yi wa wannan kotun shine ta raba aure na da matata a yau. “Anudetan ta cika bin maza kuma za ta kashe ni idan na ci gaba da zama da ita.

“Matata tana shayar da ɗiyarmu (lokacin tana wata shida) amma ta fara lalata da wani mutum da ke kusa da gidanmu. “Matar da ke da gidan ta sanar da ni abin da ke faruwa ta ce matata ta saba zuwa gidan.

“Ta shaida min cewa ta yi wa matata gargadi amma ba ta daina ba. Hakan ya sa ta karbi lambar wayata ta ce za ta kira ni duk lokacin da matata ta zo gidan.

“Kwana ɗaya bayan karɓar lambar sai naji kiran ta sai ni da ƴan uwa na muka taho a babur.

“Ta nuna mana ɗakin mutumin muke Kwankwasa ya bude muke leƙa amma ba mu ga kowa ba sai shi kaɗai.

“Har zamu tafi amma ta ce mu sake duba wa sai na koma na bincika ƙasar gado sai ga Anudetan tsirara a ƙarƙashin gado.

“A fusace na fito da ita har zan duke ta amma na daure sai dai na mata gargadin kar ta dawo gida na, na tafi na kwaso kayan ta na kai gidan saurayin nata.”

A bangarenta, wacce aka yi kara ta ce mutumin da aka gano ta a gidansa ba saurayinta bane, ta ce saurayin kawar ta ne kuma sun tafi wurinsa neman kudi ne amma kawar ta dan fita tayi wani hidima ta dawo.

Kwatsam kuma sai ka mijinta da dan uwansa sun shigo gidan suna neman cin mutuncin mutumin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here