Harkoki Sun Fara Komawa Daidai A Jihar Kano-Al’uma.

0
423
Jabiru A Hassan, Daga Kano.
AL’AMURA  sun fara komawa kamar yadda suke a fadin jihar Kano sakamakon janye dokar kulle da Gwamnan jihar Dokta Abdullahi Umar Ganduje yayi wanda kuma al’umar jihar suke bayyana ra’yoyinsu dangane da wannan umarni da Gwamna ya bayar.
Wakilin mu wanda ya duba yadda mutane suke gudanar da harkokin su, ya ruwaito cewa al’amura sun fara komawa daidai musamman ganin yadda al’uma suka fita guraren neman abincin su ba tare da wata matsala ba bayan janye dokar zama a gida na tsawon lokaci.
Haka kuma masu ababen hawa na haya da tasoshin mota da guraren cin abinci da kaauwanni duk sun kasance a bude kamar yadda aka saba wanda kuma mafiya yawan mutanen da Gaskiya Tafi Kwabo ta zanta dasu, sun bayyana cewa ko shakka babu matakin janye dokar kulle da gwamna Ganduje ya yi abune mai kyau duba da yadda annobar Covid-19 ta zamo sanadiyyar lalacewar duk wata harka a fadin duniya baki daya.
Malam Dauda Mohammed  Ali, wani direban motar haya ya shaida wa wakilinmu cewa gwamna Ganduje ya yi tunani mai kyau wajen bada umarnin janye dokar hana fita tareda jaddada cewa yanzu jihar Kano zata sake bunkasa ta fannin tattalin arziki da walwala musamman domin cike gibin da aka samu sanadiyyar cutar ta Covid-19.
Sannan ya yi fatan cewa al’uma za su ci gaba da bin dokokin kariya daga cutar ta Covid-19 ta hanyar yin amfani da umarnin da masana harkokin kiwon mafiya suka bayar domin ganin an kara dakile yaduwar cutar a fadin jihar ta kano, inda daga karshe yayi fatan cewa al’uma zasu ci gaba da gudanar da addu’oi na  kawar da wannan annoba wadda ta zamo barazana ga duniya.
Ya zuwa aiko da wannan rahoto, al’umar jihar kano sun kasance cikin yanayi na farin ciki bisa janye dokar kulle da gwamna Abdullahi Umar Ganduje yayi sannan harkoki sun fara tafiya cikin nasara musamman ganin cewa bankuna da kasuwanni da kuma harkokin sufuri sun kankama.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here