Jami’an DSS Sun Gayyaci Shugaban EFCC Ibrahim Magu

0
419
Rabo Haladu Daga Kaduna
RAHOTANNI  na cewa jami’an tsaron DSS sun ‘gayyaci’ shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC Ibrahim Magu domin yi masa tambayoyi.
Kafofin watsa labarai  sun nuna cewa jami’an tsaro sun je ofishin hukumar inda suka bukaci Mr Magu ya bi su.
Sai dai wata sanarwa da DSS ta fitar ranar Litinin ta ce ba kama Mr Magu ta yi ba.
Kakakin DSS Peter Afunanya ya ce: “DSS tana so ta shaida wa al’umma cewa ba ta kama Ibrahim Magu, mukaddashin shugaban EFCC ba, kamar yadda wasu kafafen watsa labarai suka bayar da rahoto.”
Rahotanni dai sun nuna cewa an tafi da Mr Magu fadar shugaban kasa inda ake zargin zai gurfana a gaban wani kwamiti da shugaban kasa ya kafa don duba zarge-zargen da ake yi masa na almundahana.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here