Manoma Sun Yi Kira Ga Minista Sabo Na-nono Ya Dauki Mataki Kan Rikicin Kungiyar AFAN.

0
475
Jabiru A Hassan, Daga Kano.
MANOMA a fadin kasar nan sun bukaci ministan gona Malam Sabo Na nono ya dauki mataki na gaggawa wajen magance rikicin shugabanci a kungiyar manoman Nijeriya wato (AFAN) musamman ganin yadda kungiyar take da matukar muhimmanci ga sana’ar noma.
A cikin wata ganawa da wakilin mu yayi da manoman, sun nunar da cewa yadda aka tafiya a kungiyar ko kadan babu dadi domin ana neman ruguza ta sabida son zuciya daga wasu tsirarun mutane wadanda suke da wata manufa tasu na domin ci gaba kungiyar ba, wanda kuma a Cesar manoman, yana dakyau minista Na mono ya gaggauta farfado da martabar kungiyar ta AFAN domin ci gaban manoman kasar nan.
Mazayyani Kabir Ibrahim
Alhaji Isyaku Malumfaahi daga jihar Katsina ya ce shugaban cin kungiyar manoman Nijeriya ta AFAN har yànzu yana hannun Mazayyani Kabir Ibrahim domin shi ne aka zaba bisa ka’ida amma ba wani daban ba wanda ko kadan babu wanda ya zabe shi a matsayin shugaban kungiyar illa kawai son zuciya daga wash tsirarun mutane wadanda suke da wata manufa tasu ta dàban.
Ya yi kira ga ministan gona da dukkanin masu ruwa da tsaki kan harkokin aikin gona a kasar nan da su kawo karshen rikicin shugabanci da ya dabaibaye kungiyar ta AFAN domin ganin an sami zaman lafiya da ci gaba mai albarka bisa shugabanci Alhaji Kabir Ibrahim wanda shine halastaccen shugabanci kungiyar da kowane cikakken manomi ya sani.
A nasa tsokacin manomi daga jihar Jigawa Malam Ubale na Mamuda ya Samar da cewa ” na sani cewa maigirma ministan gona Malam Sabo Na nono  ba shida masaniyar yadda aka kitsa rikicin shugabanci a kungiyar manoman Nijeriya ta AFAN ba, amma dai yana da kyau yayi bincike mai zurfi domin gano gaskiyar yadda lamarin yake ta yadda zai kawo gyara a sha’anin kungiyar”. Inji shi.
Bugu da kari, wani manomi daga jihar Kaduna Alhaji Saleh Zaria ya bayyana cewa manoman Nijeriya sun zabi Mazayyani Kabir Ibrahim a matsayin halastaccen shugaban kungiyar ta AFAN, kuma ya ce har yanzu shi ne suka sani a matsayin shugaban kungiyar tun da sai anyi zabe na gaskiya ne sannan za’a sake samun shugaba amma yadda aka bayyana wani daban ba zai taimaki kungiyar ta AFAN ba.
Daga karshe dukkanin manoman da suka tattauna da wakilin namu sun jaddada goyon bayan su ga halastaccen shugaban kungiyar ta AFAN, Mazayyani Kabir Ibrahim tare da yin kira ga ministan gona Malam Sabo Na nono da sauran kusoshin kungiyar da su gaggauta kawo karshen dàmbarwar shugabancin kungiyar gànin cewa babu wani sabbin shugaba sai Kabir Ibrahim wanda shi ne suka zaba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here