Babu Sauran Mai Dauke Da Kwayoyin Cutar Korona A Jigawa – Dakta Zakari

0
336

Daga Usman Nasidi.

MUN samu rahoton cewa, a halin yanzu babu sauran ko mutum guda mai dauke da kwayar cutar korona a jihar Jigawa da ke Arewa maos Yammacin Najeriya.

Mahukuntan lafiya a jihar sun sanar da cewa, babu sauran mai cutar a jihar.

Dakta Abba Umar Zakari, kwamishinan lafiya kuma shugaban kwamitin kar ta kwana da gwamnatin jihar ta kafa kan yaki da cutar korona, shi ne ya sanar da hakan yayin zantawa da manema labarai.

A hirarsa da manema labarai a ranar Litinin, Dakta Zakari ya ce mutum daya kacal aka samu ya kamu da cutar a duk fadin jihar cikin tsawon kwanaki 14 da suka gabata.

Mutum dayan da aka samu ya koma jiharsa ta asali inda kwararrun lafiya ke ci gaba da kulawa da shi kamar yadda kwamishinan ya bayyana.

A yayin da ya ke tabbatar da nasarar da gwamnatin jihar ta samu a fagen yaki da cutar, Dakta Zakari ya ce a halin yanzu cibiyoyin killace masu cutar da aka tanada a fadin jihar sun zama fayau babu kowa a cikinsu.

Rahotanni sun bayyana cewa, bayan fiye da watanni hudu da bullar cutar korona karo na farko a Najeriya, cutar ta yadu a jihohi 36 da kuma babban birnin kasar na Tarayya wato Abuja.

Wannan ya na kunshe cikin kididdigar alkaluman da Hukumar Dakile Cututtuka Masu Yaduwa a Najeriya NCDC ta fitar a daren ranar Litinin, 6 ga watan Yuli.

Taskar bayanai ta NCDC ta nuna cewa, babu jihar da ba a samu bullar cutar ba a duk fadin kasar, inda a baya bayan nan aka gano masu dauke da kwayoyin cutar karo na farko a jihar Kuros Riba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here