Canji Yanayi: Mai Martaba Sarkin Fika Emir ya Roki Gwamnnatin Jihar Yobe Da Ta Samar Da Hukunci Ga Masu Sare Itatuwa Ba Izini

0
348

Muhammad Sani Gazas Chinade, Daga  Damaturu

MAI martaba Sarkin Fika kuma shugaban majalisar sarakunan Jihar Yobe Dr Muhammad Ibn Abali Muhammad ya roki gwamnatin Jihar da ta samar da wata dokar da ke dauke da hukunci mai tsanani ga duk mutumin ko mutanen da ke sare itatuwa ba izini.
Sarkin na Fika ya yi wannan roko ne lokacin da ya ke karbar bakuncin kwamishinan ma’aikatar kula da muhallin Jihar ta Yobe Alhaji Yakubu Sidi Karasuwa bisa ziyararsa ga sarakuna iyayen kasa da ya ke kaiwa kan batun kula da dasa itatuwa don’t inganta muhalli.
Basaraken ya kara da cewar, wannan ziyara da kwamishinan kula da muhalli ya kawo wannan masarauta ya zo ne dai-dai da lokacin da wasu al’ummomin masarautar da ma na wassu banagarorin Jihar suka hadu da iftila’in  ta’adin ruwa da iska da ya lalata gidajensu da kuma wadda kadarorinsu.
Don haka Basaraken ya jaddada bukatar su ta wajen kafa dokokin da za su hana sare bishiyoyi a fadin Jihar da wassu ke yi don Samar da makashin girki wadda hakan ba karamin illa ya me yiwa muhalli ba.
“Za mu ci gaba da wayar da kan jama’armu dangane da illar yin hakan musamman wajen canja tunaninsu kan hakan, don ingantuwar muhallin mu” in ji Basaraken.
Run farko da ya ke jawabi, kwamishina ma’aikatar kula da muhallin Alhaji Yakubu Sidi Karasuwa  ya bayyana cewar, sun ziyarci fadar ta Fika ne bisa umarnin da Gwamna Mai Mala ya basu Na mika sakonni garesu iyayen kasa dangane da matsalolin  da muhalli ke fuskanta  don  amfanin gaba.Kwanishinan ya kuma yabawa Mai Martaba Sarkin na Fika bisa kokarinsa na yaki da sare itatuwa a masarautarsa da ma Jiha baki daya.
A cewarsa, a wannan sheakara sun Samar da itatuwa akalla Miliyan 3 don dasawa a dukkan fadin Jihar.Alhaji Yakubu Sidi ya jaddada kudirin gwamna Mai Mala wajen ganin an kawo karshen sare itatuwa barkatai a Jihar wadda kan haifar da illa ga muhalli musamman kan dimamar muhalli.Don haka ne kwamishinan ya roki jama’a da su rika Shuka itatuwa a gidaje da gonakensu da kuma gefen tituna tare da nuni da cewar, nan ba da dadewa bane gwamnatin Jihar za ta Samar da ishasshen irin shukawa ga al’umma.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here