Hukumar NSCDC Ta Kama Shugaban Kungiyar Miyagu Ta Shila A Adamawa

0
367

Daga Usman Nasidi.

HUKUMAR Jami’an Tsaro ta NSCDC reshen jihar Adamawa ta kama hatsabibin shugaban kungiyar Miyagu ta Shila, Micheal Linus.

Mista Nuradeen Abdullahi, Kwamandan Rundunar ta jihar ya gabatar wa manema labarai wanda ake zargin a ranar Talata a Yola.

Abdullahi ya ce rundunar ta hanyar tattara bayanin sirri ta kama Linus da aka fi sani da Damudu, shugaban kungiyar miyagu ta Shila da wasu miyagun biyu da rundunar ta dade tana nema.

Kwamandan ya yi bayanin cewa kafin kama shi, Linus gawurtaccen wanda ake zargi da aikata laifi ne da ya kasance yana fitinar mutanen jihar.

“Mun dade muna neman Micheal Linus, mai shekara 22. Ya kware wurin aikata laifuka karkashin kungiyar Shila, koyar da kananan yara miyagun ayyuka da sayar da muggan kwayoyi.

“Bayanan da muke da shi sun nuna cewa wanda ake zargin ya yi wa mutane da dama rauni a jihar.

“Sauran wadanda ake zargi da laifin sun hada da, Mohammed, mai shekara 33, dan kwangilar bogi da ya kware wurin zuwa makarantun gwamnati a kauyuka yana gabatar da kansa a matsayin dan kwangila.

“Ya kware wurin satar rufin gidaje. Ya kan rudi yan kauyen cewa an bashi kwangilar canja rufin makarantu idan ya cire sai ya tafi ya siyar, ” in ji Abdullahi.

Ya ce na ukun kuma wani Mustapha Ismail ne da ake zarginsa da satar motocci da kayan mutane.

Asirin Abdullahi ta tonu ne lokacin da aka kama shi yana kokarin kwace wa wani mota kuma aka karbo motar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here