‘Yan Fashin Daji Sun Sake Kai Farmaki A Kauyukan Zamfara Da Sakkwato

0
767

Rahoton Z A Sada

ƊIMBIN mutane ne rahotanni suka ce sun tsere daga gidajensu sakamakon hare-haren ‘yan fashin daji a yankunan Isan jihar Sokoto da ma na Zamfara mai maƙwabtaka tun daga farkon wannan mako.

Bayanai daga ƙaramar hukumar Shinkafi sun ce gomman mutane ne suka fantsama manyan garuruwan yankin kamar ita Shinkafin don kuɓuta da rayukansu.

Wata shaida da ta tsere daga ƙauyen Kamarawa ta faɗa wa BBC daga inda ta fake a cikin daji cewa sun baro gidajensu ne lokacin da suka ga mahara na far wa mazajensu tare da yin awon gaba da dabbobi.

“A jiya (Litinin) da safe, sai muka ga jiragen sama suna ta yawo a yankinmu, sai suka sauka jejin da ɓarayin suke, suna ta sako musu bom-bom da bindigogi. Ga sojoji daga sama suna ta yin shuuu,” in ji matar.

Ta ce sun yi ta murna don kuwa suna tunanin wahala ta yanke musu. “Muna cewa ƙila za a ɗauke mana mutanen nan ne.”

Sai dai ta ce lafawar da aka samu ta jami’an tsaron sai ‘yan fashin dajin da suka noƙe suka sake far wa ƙauyukan yankin. Ta ce daren jiya (Litinin) ƙauye uku suka tayar.

“Ka ga asibitin Shinkafi, akwai mutane kwakkwance, asibitin Isa, akwai mutane kwakkwance. Yanzu kuma yau (Talata) Kamarawa, tun da mangariba suka shiga, sun gewaye ta gaba ɗaya,” in ji shaidar.

Maharan dai sun kai hare-haren ne a kan babura inda suka riƙa harbi kan mai uwa da wabi.

Lamarin na zuwa ne daidai lokacin da mutanen ƙauyen Danfasa cikin ƙaramar hukumar Maru a Zamfara ke juyayin sace mata 20 da kuma mutum bakwai da aka kashe a wani hari da yammacin ranar Litinin.

Wani mutumin ƙauyen ya faɗa yayin zantawa ta wayar tarho cewa suna tsakiyar cin kasuwa a wani ƙauye mai maƙwabtaka da su ne ranar Litinin lokacin da maharan suka far wa gidajensu a Danfasa da yamma.

A cewarsa, baya ga mutanen da aka jikkata, an kuma kashe mace biyu da namiji biyar cikinsu har da dattijai guda biyu.

Sojojin NajeriyaHakkin mallakar hotoNIGERIAN ARMY
Rundunar sojan Najeriya ta ce ta lalata sansanonin ‘yan fashin daji da dama

Shaidan wanda ya ce an ƙone kusan rabin ƙauyensu, ya ce a halin da yake magana ma yana kan hanyarsa ne ta barin yankin saboda rashin tabbas a garuruwansu.

Ya ce daga ciikin mata ashirin da ‘yan fashin suka sace har da ‘yarsa mai kimanin shekara talatin, ya kuma ce har yanzu ba su ji amo ko labarinsu matan ba.

Mutumin ƙauyen Ɗanfasa ya kuma koka kan rashin kai musu ɗauki don kuɓutar da iyalinsu da dukiyarsu daga maharan, duk da neman gudunmawar da suka yi a wajen hukumomi.

Jihohin Zamfara da Sokoto da Katsina dai sun daɗe suna fama da hare-haren ‘yan fashin daji, duk da matakan da gwamnatin Najeriya kan ce tana ɗauka don kawo ƙarshensu.

A baya-bayan nan ma sai da Shugaba Muhammadu Buhari ya bai wa al’ummar jihar Katsina haƙuri tare da cin alwashin ɗaukar ƙwaƙƙwaran mataki don murƙushe ‘yan fashin da suka addabi sassan yanki.

Zuwa yanzu dai jami’an tsaron Najeriya ba su tabbatar ko musanta rahotannin kai wadannan hare-hare ba.

Kuma ga alama sai nan gaba ne za a iya tantance irin ɓarnar da maharan suka haddasa a ƙauyukan da suka far wa musamman na baya-bayan nan garin Kamarawa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here